Isa ga babban shafi

MDD ta ce akwai bukatar wadata Gaza da kayayyakin agaji saboda halin da suke ciki

Majalisar dinkin duniya ta bukaci a samar da wadataccen kayayyakin agaji a Gaza duba da yanayin kunci da al'umar suka samu kansu a ciki.

Magatakarda na MDD, António Guterres.
Magatakarda na MDD, António Guterres. REUTERS/Lucas Jackson
Talla

Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya bayyana cewa lokaci ya yi da za a cika Gaza da kayakin agaji, a yayin da bayyana cewa bai kamata ace wannan yankin ya kasance cikin muguwar yunwa ba.

Guterres Ya kuma bukaci a tsagaita bude wuta nan take tsakanin Isra'ila da Hamas.

Sakatare janar din ya yi Magana ce a gefen kan iyakar Masar da ke kusa da birnin Rafah da ke kudancin Gaza, inda Isra'ila ke shirin kai farmaki ta kasa duk da gargadin da ake yi na cewa za a iya fuskantar bala'I a wannan yankin da fiye da rabin al'ummar Gaza suka samu mafaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.