Isa ga babban shafi

An jinkirta kuri'ar MDD na neman tsagaita wuta a Gaza saboda jan kafar Amurka

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya sake jinkirta zaman kada kuri’ar kan bukatar tsagaita wuta a zirin Gaza zuwa wannan Laraba, domin lallabar Amurka da ke jan kafa kada ta sake hawa kujerar naki, a daidai lokacin da ayyukan agaji ke dab da durkushewa da kuma tabarbarewar tattalin arzikin duniya.

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya sake jinkirta zaman kada kuri’ar kan bukatar tsagaita wuta a zirin Gaza zuwa yau Laraba 20/12/23
Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya sake jinkirta zaman kada kuri’ar kan bukatar tsagaita wuta a zirin Gaza zuwa yau Laraba 20/12/23 © Shannon Stapleton / Reuters
Talla

Wata majiyar diflomasiyya ta ce, an sake dage zaman kada kuri’ar da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kan kudurin tsagaita wuta a zirin Gaza, saboda bangarori da dama na ci gaba da tattaunawa domin kada Amurka ta mamaita hawa kujerar naki.

A yayin da ake ci gaba da kiraye-kirayen a cimma sabuwar yarjejeniyar, wata majiya ta tabbatar da cewa, shugaban kungiyar Hamas na kasar Qatar Ismail Haniyeh zai ziyarci Masar a wannan Laraba domin tattaunawa kan tsagaita wuta a Gaza da kuma musayar fursunoni da Isra'ila.

A Gazan, mazauna garin Khan Younis sun ce ana gwabza  kazamin fada tsakanin mayakan Hamas da sojojin Isra'ila a tsakiya da kuma gabashin gundumomin kudancin birnin.

Hari cikin Isra'ila

Wasu sabbin bayanai kan harin da Hamas ta kai cikin Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba sun tabbatar da girman tashin hankalin da ba a taba ganin irinsa ba, wanda ke  kalubalantar wasu shaidun farko.

Adadin wadanda suka mutu a harin ya zuwa yanzu ya kai 1,139, daga cikinsu fararen hula Isra'ila 695 da suka hada da yara 36, jami'an tsaro 373 da kuma baki 71. Adadin da aka yi wa gyaran fuska bai hada da wasu mutane biyar ba wato hudu daga cikinsu Isra’ila, wadanda har yanzu ofishin firaministan kasar ya lissafa a matsayin wadanda ba a san su ba.

Adadin Gaza

Akalla mutane 19,667 ne suka mutu a harin da Isra’ila ta kai a Zirin Gaza, yayin da wasu 52,586 suka samu raunuka, a cewar ma’aikatar lafiya a yankin da Hamas ke mulki. Akalla mutane 7,600 ne suka bata, a cewar ofishin yada labaran Hamas.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.