Isa ga babban shafi
Yakin Gaza

Kwamitin Tsaro na kada kuri'a kan tsagaita wuta a Gaza

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya na kada kuri’a a wannan Litinin kan wani kudiri da ke bukatar Isra’ila da Hamas su tsagaita bude wuta don samun damar shigar da kayayyakin agaji cikin Zirin Gaza ta kan iyakokin kasa da ruwa da kuma ta sama.

Wani zama na Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya
Wani zama na Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya AP - Seth Wenig
Talla

Jami’an diflomasiya sun ce, makomar wannan kudirin da aka shata a Kwamitin Tsaron na Majalisar Dinkin Duniya na fuskatar barazana, lura da cewa, a can baya, Amuka ta yi amfani da karfin kujerarta wajen dakile cimma jituwar.

Duk wani kudiri dai na Kwamitin Tsaron na bukatar akalla kuri’un kasashe 9 ba tare da samun wata kasar da ta hau kujerar na ki ba daga cikin kasahen Amurka da Faransa da China da Birtaniya da kuma Rasha kafin amincewa da shi.

A bangare guda, a wannan Litinin din ne ake sa ran Ministar Harkokin Wajen Faransa, Catherine Colonna za ta isa Lebanon duk dai don tattaunawa kan batun tsagaita bude a kan iyakar Isra’ila.

Uwargida Catherine za ta gana da Firaministan Lebanon Najib Mikati da kuma kakakin majalisar dokokin kasar, Nabih Berri, wanda babban amini ne ga kungiyar Hezbollah mai samun goyon bayan Iran.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da ragargazar Gaza a yau Litinin duk kuwa da caccakar da masu rajin kare hakkokin bil’adama ke yi wa kasar na cewa, da gangan take jefa Falasdinawa cikin yunwa da sunan yaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.