Isa ga babban shafi

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci tsagaita wuta a Gaza

Wani kudirin da kasar tsibirin Malta ta gabatar ga komitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya samu amincewar kuri’un mambobin 12 daga cikin 15 a yayin da 3 suka kauracewa zaben, wato Amurka da Inglila da kuma Rasha.« Kiran na samar da turbar ayukan jinkai na yan kwanaki ana bukatar ganin ya tabbata cikin gaggawa »  domin bada damar isar da kayayyakin jinkai ga fararen hular dake yankin Gaza.

Ambassador Riyad Mansour, Permanent Observer of the State of Palestine to the United Nations waits to speak during an emergency meeting of the UN security council regarding the situation in Palestine, at UN headquarters in New York City on January 5, 2023. - Israel's ambassador to the UN slammed a Security Council meeting on the controversial visit to Jerusalem's Al-Aqsa mosque compound by an Israeli minister as "pathetic" and "absurd" Thursday. (Photo by TIMOTHY A. CLARY / AFP)
Ambassador Riyad Mansour, Permanent Observer of the State of Palestine to the United Nations waits to speak during an emergency meeting of the UN security council regarding the situation in Palestine, at UN headquarters in New York City on January 5, 2023. - Israel's ambassador to the UN slammed a Security Council meeting on the controversial visit to Jerusalem's Al-Aqsa mosque compound by an Israeli minister as "pathetic" and "absurd" Thursday. (Photo by TIMOTHY A. CLARY / AFP) AFP - TIMOTHY A. CLARY
Talla

Ita dai wannan bukata ta dora ayar tambaya kan yawan kwanakin da za su isa wajen gudanar da aikin jinkan isara da kayayakin bukatun rayuwa ga fararen hular yankin  Gaza, dake ci gaba  shan ukuba daga  Isaraela.

kudirin da kamfanin dillancin labaran AFP ya samu damar lekawa, ya bukaci ganin, Israela ta dakatar da barin wutar da take ci gaba a yi kan rayukan falestinawa na tsawon kwanaki 5, da zai fara aiki a cikin awanni 24 bayan kada kuriar amincewar da shi.

 « Ya kamata kudirin ya kasance mai tsawo, domin bada damar tattara kayyakin aikin, da zasu bada damar cimma burin da aka sa gaba da zarar an samu makamashin man fetur domin isarwa al’umma abinda suke bukata »,  a cewar Stéphane Dujarric, kakakin babban sakataren  Majalisar Dinkin Duniya, da bai yi wani  karin haske a kai ba.

Kudurorin komitin tsaro na MDD dai masu  tsauri ne da suka kunshi dokokin duniya, wandan ke tilasatawa duk wata kasa dake mambar Majalisar da ta mutunta su, kamar yadda mambobin suka yi kiran yi, a cewar wakilin RFI New York, Carrie Nooten. Kafin karshen zaman taron dai, Isaraela ta bayyana aniyarta na ci gaba da fadan da  take ta hanayar « mutunta dokokin duniya». 

Kudirin, da ya nanata mawuyacin halin da hare haren na Isaraela suka jefa  kananan yara a ciki, « ya bukaci dukkanin bangarorin biyu da su mutunta wannan umarni dake karkashin dokokin duniya, musaman abinda ya shafi kare rayukan fararen hula musaman yara kankana  ».

« Har i la yau Majalisar ta Dinkin Duniya ta yi kiran ganin an saki daukacin yahudawan da Hamas da wasu kungiyoyin Falestinawa ke garkuwa da su nan take», ba tare da yin tir ko zargin  Hamas kan harin da ta kai kan Israela na ranar 7 ga watan octoban 2023 da ya yi sanadiyar kisan yahudawa dubu 1.200 a cewar mahukumtan Falestinawa.

« yara dubu 5 000 ne Izraela ta kashe a Gaza: wannan ya kasance wata alma ce dake kan goshin komitin tsaron. Ya kamata a ceta yi wani abu tun farkon ballewar yakin… amma ta ko wane hali muna bukatar ganin mun ceto rayukan daruruwan  yara da fararen hular da suka yi saura a gaza.

A kan haka ne wannan kudiri ya kara samar da dan ci gaba kan kyakywar alkibla.

A nasa bangaren jikadan  Palestinu a MDD Riyad Mansour ya ce, Duk da cewa,  babu wata yarjejeniyar tsagaita wuta da aka nema, amma ci gaba ne kudirin na jiya da aka samar ta wannan fanni»,

Shiru  ba aiki

Komitin tsaron na Majalisar Dinkin Duniya kumya kumaya  ya jaraba yin magana da murya guda, bayan harin da Hmas ta kai da kuma rusa ginigine da kashe rayukan mutanen da Izzraela ke yi a Gaza.

Inda hare haren bama-baman da Isareala ke kaiwa babu kakkautawa  ta jiragen sama kan Gaza su ka yi sanadiyar mutuwar akalla sama da falestinawa dubu 11 500, da suka hada da yara dubu  4 710 in ji ma’aikatar ministan kiyon lafiyar Hamas.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.