Isa ga babban shafi

Lokaci na kurewa kan bukatar dakile kisan kare dangi a Gaza - MDD

Wasu kwararrun jami’ai masu zaman kansu na Majalisar Dinkin Duniya, sun bukaci a gaggauta tsagaita wuta a Zirin Gaza, inda suka yi gargadin cewa lokaci na kurewa kasashe kan bukatar dakile aikata kisan kare dangin da ake yi wa Falasdinawa a yankin na Gaza.

Wani Bafalasdine cikin jimami, bayan harin Isra'ila da ya kashe Falasdinawa a sansanin 'yan gudun hijira na Jabaliya da ke Zirin Gaza.
Wani Bafalasdine cikin jimami, bayan harin Isra'ila da ya kashe Falasdinawa a sansanin 'yan gudun hijira na Jabaliya da ke Zirin Gaza. REUTERS - Stringer .
Talla

Bayan shafe kusan makwanni hudu tana luguden bama-bamai a Gaza da nufin murkushe mayakan Hamas, alkaluma sun nuna cewar zuwa yanzu, Isra’ila ta kashe Falasdinawa sama da dubu 9,000, fiye da rabinsu kuma mata ne da kananan yara.

Kasar ta Isra’ila dai na ci gaba da nanata cewar, tana kai hare-haren ne kan mayakan Hamas, wadanda take zargi da yin amfani da fararen hula a matsayin garkuwa.

A tsakanin ranakun Talata da Larabar da suka gabata, mutane kusan 200, Isra’ila ta kashe yayin hare-hare  sau biyu da ta kai kan sansanin Falasdinawa ‘yan gudun hijira mafi girma a Gaza na Jabaliya.

A baya bayan nan ne dai Hadaddiyar Daular Larabawa ta ce za ta kula da lafiyar Falasdinawa yara dubu 1000, wadanda hare-haren Isra’ila suka jikkata a Zirin Gaza.

Sai dai gwamnatin Daular Larabawan ba ta fayyace yadda za a yi ta kwaso yaran kanana daga yankin na Gaza ba, wanda Isra’ila ta killace yau da tsawon kusan makwanni hudu, bayan kaddamar da hare-haren ramuwar gayya kan farmakin da mayakan Hamas suka kai mata a ranar 7  ga watan Oktoba, inda suka kashe mutane fiye da 1,400.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.