Isa ga babban shafi
Isra'ila - Gaza

Isra'ila na ci gaba da luguden wuta ta ƙasa da sama kan Gaza

Isra’ila ta ci gaba da ruwan bama-bamai a Gaza da manyan bindigogi da kuma hare-hare ta sama a yau Juma’a a matsayin martani ga rokoki da aka harba mata daga yankin da ke karkashin ikon Hamas, a rikicin da ke kara muni wanda ya zuwa yanzu ya hallaka sama da Falasdinawa 100.

Tsohon hoton rikicin Isra'ila da Hamas na ranar 5 ga watan Yuni shekarar 2014
Tsohon hoton rikicin Isra'ila da Hamas na ranar 5 ga watan Yuni shekarar 2014 AP - Tsafrir Abayov
Talla

Majalisar Dinkin Duniya ta ce Kwamitin Tsaron zai yi zama a ranar Lahadi don lalubo hanyar magance rikicin kamar yadda Sakatare Janar na Majalisar Antonio Gutteres ya yi kira da "a hanzarta kawo karshen mamaye da kuma dakatar da fada".

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya ce Washington "ta damu matuka game da tashin hankalin da ake yi, kuma Ma'aikatar Harkokin Wajen ta bukaci 'yan kasar da su "sake tunani game da tafiya zuwa Isra'ila".

Kamfonin sufurin sama sun dakatar da jiragensu

Yawancin kamfanonin jiragen sama na duniya - ciki har da KLM, British Airways, Virgin, Lufthansa da Iberia - sun soke tashin jirage a sakamakon yadda ake kai hare-hare ta sama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.