Isa ga babban shafi

Jami'in MDD yayi murabus don barranta da kashe dubban Falasdinawa a Gaza

Babban daraktan ofishin kare hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York Craig Mokhiber, ya yi murabus daga mukaminsa, sakamakon kisan kare dangin da ya ce Isra’ila na yi a Zirin Gaza.

Zauren Majalisar Dinkin Duniya
Zauren Majalisar Dinkin Duniya AP - Mary Altaffer
Talla

Cikin budaddiyar wasika mai tsawo da ya rubuta, Craig ya bayyana takaicin ganin yadda Majalisar Dinkin Duniya ta kasa tabuka komai wajen dakatar da ta’asar da yace Isra’ila na yi a Gaza.

Jami’in ya kuma yi Allah wadai da matsayar da gwamnatin Amurka da kuma wasu kafofin yada labaran kasashen yamma suka dauka a kan abinda ke faruwa a yankin na Gaza da sunan yaki tsakanin Isra’ila da Hamas.

A ranar Larabar nan ne dai, shugaban hukumar kula da Falasdinawa ‘yan gudun hijira Philippe Lazzarini, ya ce majalisar Dinkin duniya za ta ci gaba da tallafa wa fararen hular da ke Zirin Gaza,

Babban Jami’in ya sha alwashin ne yayin ziyarar da ya kai zuwa yankin, inda ya bayyana kaduwa kan halin tagayyarar da fararen hula ke ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.