Isa ga babban shafi

Masu zanga-zanga sun yi kokarin katse zaman majalisar Amurka kan taimaka wa Isra'ila

Masu zanga-zanga a Amurka sun yi ta kokarin katse zaman majalisun dokokin kasar da ya gudana a jiya Talata, a yayin da biyu daga cikin manyan mashawartan shugaba Joe Biden suka sun bukaci amincewar 'yan majalisar kan shirin baiwa Isra’ila tallafin karin biliyoyin daloli.

Wasu Amurkawa da suka rina hannayensu da launin jini tsaye a bayan sakataren harkokin waje Antony  Blinken a zauren majalisar dokokin Amurka, domin nuna adawa da hare-haren Isra'ila kan Zirin Gaza.
Wasu Amurkawa da suka rina hannayensu da launin jini tsaye a bayan sakataren harkokin waje Antony Blinken a zauren majalisar dokokin Amurka, domin nuna adawa da hare-haren Isra'ila kan Zirin Gaza. REUTERS - KEVIN LAMARQUE
Talla

Dandazon fusatattun mutanen da suka mamaye harabar gaban ginin majalisun na Amurka, yayin da wasu suka samu shiga cikin zauren majalisar, sun yi ta furta kalaman yin tir da jami’an gwamnatin kasar da suka ce suna goyon bayan kisan kare dangin da Isra’ila ke yi wa fararen hula a Gaza.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar da suka rina hannayensu da launin ja mai alamun jini, sun rika kokarin hana jami'an gwamnatin na Amurka jawabi.

Wata Ba'amurkiya mai zanga-zangar yin Allah wadai da Isra'ila, yayin da jami'an tsaro ke kokarin fitar  da ita daga zauren majalisar dattijan Amurka. 31, Oktoba 2023.
Wata Ba'amurkiya mai zanga-zangar yin Allah wadai da Isra'ila, yayin da jami'an tsaro ke kokarin fitar da ita daga zauren majalisar dattijan Amurka. 31, Oktoba 2023. REUTERS - KEVIN LAMARQUE

Yayin da suka bayyana gaban kwamitin kasafin kudin majalisar dattawa, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken da sakataren tsaro Lloyd Austin sun bayyana cewar shugaba Biden na bukatar dala biliyan 106, kudaden da suka ce daga cikinsu zai bai wa Ukraine dala biliyan 61, sai dala biliyan 14 ga Isra'ila, dala biliyan 9 kuma don gudanar da ayyukan agaji Zirin Gaza da Isra’ila.

Ragowar ayyukan da za yi da sabon kasafin sun hada da kashe dala biliyan 13 wajen inganta tsaro a iyakokin Amurka da kuma dala biliyan 4 da za a kashe don dakile tasirin kasar China a nahiyar Asiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.