Isa ga babban shafi

Hamas ta saki Amurkawa biyu da ta yi garkuwa da su

Hamas ta saki wasu Amurka biyu, Judith Tai Raanan da ‘yarta mai shekaru 17, Natalie Raanan a ranar Juma’a, kusan makwanni biyu bayan kaddamar da mummunan hari a kan Isra’ila, inda ta yi garkuwa da kimanin mutane 200.

Amurkawa, Judith Tai Raanan (tsakiya) da 'yarta  Natalie, wadanda Hamas ta sake. 20 ga watan Oktoba, 2023.
Amurkawa, Judith Tai Raanan (tsakiya) da 'yarta Natalie, wadanda Hamas ta sake. 20 ga watan Oktoba, 2023. © REUTERS/Al-Qassam brigades
Talla

Kakakin ma’aikatar tsaron Isra’ila, Daniel Hagari ya mika wadannan Amurkawa biyu ne ta kan iyakar Gaza, kuma yanzu su na karkashin kulawar rundunar tsaron Isra’ilar.

Wadannan Amurkawan da aka saki ‘yan jihar Chicago ne na Amurka, kuma sun ziyarci ‘yan uwansu ne a garin Nahal Oz da ke kudancin Isra’ila lokacin da suka gamu da wannan alkaba’i a ranar  7 ga watan Oktoba.

Mahukuntan Isra’ila sun ce mutane dubu 1 da dari 4 ne suka mutu, da suka hada da fararen hula da sojoji a yayin harin da Hamas ta kai, wanda ya kasance mafi muni da kasar ta taba fuskanta tuun bayan kafa ta shekaru 75 da suka wuce.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.