Isra'ila ta kai hari mafi muni a Gaza tun soma rikicinta da Hamas
Dakarun Isra’ila sun ci gaba ruwan bama-bamai a zirin Gaza a Litinin din nan, bayan da aka gaza a kokarin da ake na barin masu rike da fasfunan kasashen waje ficewa, tare da isar da kayayyakin agaji ga masu bukata a yankin na Falasdinu.
Wallafawa ranar:
Mazauna yankin zirin Gaza, wanda ke karkashin ikon kungiyar Hamas sun ce luguden wutar da aka yi cikin daren Lahadi shi ne mafi muni a wannan rikici da aka shafe tsawon kwanaki 10 ana yi, a ya yin da ake ganin ba makawa Isra’ila na shirin kutsawa yankin ta kasa.
Rahotanni na cewa an ci gaba da luguden wuta ba kakkautawa a wannan rana ta Litinin, abin da ya rushe gine-gine da dama, mutane da dama kuma suka makale a cikin baraguzai.
Ana ta kokari ta hanyar diflomasiya don isar da kayayyakin agaji wannan yankin da ya ke ta fuskantar dirar mikiya daga Isra’ila tun bayan harin da kungiyar Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoban nan, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane dubu 1 da dari 3, asara mafi muni da kasar ta taba fuskanta a cikin shekaru 75 bayan kafuwarta.
Dimbim kayayyakin agaji daga kasashe da dama ne suka makale a Masar, a ya yin da ake jiran yarjejeniyar da za ta bayar da damar isar su Zirin Gaza tare da kwashe masu rike da fasfunan kasashen waje ta kan iyakar Rafah.
Tun da farko a wannan Litinin, majiyoyin tsaron sun bayyyana cewa an cimma yarjejeniyar bude wannan iyaka domin kayayyakin agaji su isa ga wadanda ke bukata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu