Isa ga babban shafi

Shugaban Hamas ya zargi Isra'ila da aikata laifukan yaki a Gaza

Shugaban kungiyar Hamas Isma'il Haniyeh, ya zargi Isra'ila da aikata laifukan yaki, a yayin da sojojin kasar ke ci gaba da kai hare-hare ta sama a Zirin Gaza, tare da shirye-shiryen kaddamar farmaki ta kasa da nufin murkushe mayakan kungiyar ta Hamas

Shugaban kungiyar Hamas Isma'il Haniyeh
Shugaban kungiyar Hamas Isma'il Haniyeh REUTERS - AZIZ TAHER
Talla

Haniyeh, ya yi Allah wadai da zaluncin na Isra'ila ne a cikin wata wasika da ya aike wa sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, wadda aka wallafa a shafin Intanet na kungiyar Hamas.

Shugaban na Hamas da a yanzu haka ke zaune a kasashen waje, ya bukaci Guterres da ya matsa wa Isra'ila, domin ta bayar da damar shigar da kayan agaji cikin Gaza, inda ya zuwa yanzu take ci gaba da katsewa samun ruwan sha, da abinci da kuma wutar lantarki.

A cikin wata sanarwa ta daban, Hamas ta bukaci kungiyoyin agaji da na kasashen Larabawa da na sauran kasashen Musulmi da su tallafa wa asibitocin Gaza da ke fama da tarin kalubale.

Kimanin Falasdinawa miliyan 2 da dubu 400 ne ke zaune a Zirin Gaza, wanda ke karkashin takunkumin kawanyar Isra'ila tun bayan da Hamas ta karbe iko da shugabancin yankin a shekarar 2007.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.