Isa ga babban shafi

Saudiya ta dakatar da tattaunawa da Isra'ila kan daidaita alaka tsakaninsu

Saudiya ta dakatar da tattaunawa kan shirin maido da alakar diflomasiya tsakaninta da Isra'ila, a daidai lokacin da ake ci gaba da yaki tsakanin Isra'ilar da kungiyar Hamas ta Falasdinu wanda ke kara rincabewa.

Benjamin Netanyahu (dama) yayin taron jam'iyyar Likud a birnin Kudus, ranar 13 ga Disamba, 2021; da kuma Yarima mai jiran gado na Saudiya Mohammed bin Salman yayin jawabi a taron koli na kasashen yankin Gulf a birnin Riyadh. 14 ga Disambar 2022.
Benjamin Netanyahu (dama) yayin taron jam'iyyar Likud a birnin Kudus, ranar 13 ga Disamba, 2021; da kuma Yarima mai jiran gado na Saudiya Mohammed bin Salman yayin jawabi a taron koli na kasashen yankin Gulf a birnin Riyadh. 14 ga Disambar 2022. © Yonatan Sindel/Flash90; Bandar Aljaloud/Saudi Royal Palace via AP
Talla

Wata majiya ta ce tuni masarautar Saudiyan ta sanar da jami’an Amurka matakin da ta dauka.

A makwannin da suka gabata Saudiya ta fara tattaunawa da Isra’ila wadda Amurka ta kulla da zummar daidaita hulda a tsakanin kasashen biyu.

A karshen makon nan gwamnatin Saudiyan ta yi amfani da kakkausan harshe wajen caccakar Isra’ila kan hare-haren da take kaiwa a Zirin Gaza, da zummar murkushe mayakan Hamas, inda fararen hula sama da dubu 1 da 500 suka rasa rayukansu.

A ranar Juma'a ne Saudiya ta kuma yi Allah wadai da umarnin yin gudun hijirar da Isra’ila ta bai wa Falasdinawa sama da miliyan 1, wadanda a yanzu suke kokarin komawa zuwa kudancin yankin daga arewacinsa don tsira da rayukansu, kafin Isra’ilar ta kaddamar da farmaki ta kasa.

A ranar 7 ga watan Oktoba kungiyar Hamas ta kaddamar da wani gagarumin hari kan Isra'ila wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 1,300, lamarin da ya janyo hare-haren ramuwar gayya da a cikinsu, Isra’ila ta jefa bama-bamai sama da dubu 6000 kan Falasdinawa a arewacin Gaza, inda mutane akalla 1,900 suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.