Isa ga babban shafi

Saudiya da Iran sun sha alwashin shiga tsakani a yakin Hamas da Isra'ila

Kasashen Saudiya da Iran sun tattauna da juna game da yakin da ya barke tsakanin Isra’ila da Hamas da zuwa yanzu ya kasha mutanen da yawansu ya tasamma dubu 2 da 500 a bangarorin biyu baya ga jikkata dubbai.

Yadda Isra'ila ta yi luguden wuta kan yankin Gaza.
Yadda Isra'ila ta yi luguden wuta kan yankin Gaza. REUTERS - MOHAMMED SALEM
Talla

Majiyoyin sun tabbatar da doguwar tattaunawa ta wayar tarho tsakanin shugaba Ebrahim Raisi na Iran da Yarima mai jiran gadon sarautar Saudiya Mohammed bin Salman a kiran wayar da ke matsayin karon farko tsakanin jagororin biyu tun bayan dawo da hulda tsakaninsu cikin watan Maris.

Mashawarci na musamman ga fadar shugaban kasar Iran kan harkokin siyasa, Mohammad Jamshidi a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, ya ce bangarorin biyu sun amince da shiga tsakani don kawo karshen luguden wutar sojin Isra’ila a yankin Gaza.

Kamfanin dillancin labarai na Saudiya SPA ya ruwaito cewa Yarima Mohammed bin Salman ya sha alwashin tabbatar da wadatuwar kayakin agaji a yankin na Gaza.

Salman ya kuma bayyana cewa Saudiya za ta yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin ta kawo karshen yakin wanda ke shiga kwana na biyar a yau Alhamis, bayan da Hamas ta kaddamar da hare-hare ta ruwa da sama da kuma sararin Samaniya kan kasar ta Yahudawa.

Zuwa yanzu Falasdinawa fiye da dubu 1 da 200 Isra’ila ta kashe a luguden wutar da ta yi wa yankin Gaza, inda a bangare guda Hamas ta kashe Yahudun Isra’ila akalla dubu 1 da 300.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.