Isa ga babban shafi

Hamas ta yi barazanar kashe ilahirin mutanen da ta kama a Isra'ila

Kungiyar Hamas ta yi barazanar kashe ilahirin mutanen da ke hannunta, wadanda ta kama a hare-haren da ta kaddamar kan Isra’ila ranar Asabar, matukar kasar ba ta dakatar da hare-hare tare da kawanyar da ta ke yiwa yankin Gaza ba, wannan ikirari dai na zuwa a dai dai lokacin da shugaba Joe Biden ke cewa akwai fargabar har da Amurkawa cikin mutanen da ke hannun kungiyar.

Wasu mayakan Hamas a Gaza.
Wasu mayakan Hamas a Gaza. AP - John Minchillo
Talla

Barazanar ta Hamas na zuwa ne bayan Isra’ila ta kammala yiwa yankin na Gaza kawanya a jiya Litinin, tare da katse lantarki da ruwa baya ga hanyoyin shigar da abinci, lamarin da ya sanya fargabar tabarbarewar lamurran jinkai a yankin mai fama da tarin mutanen da Isra’ila ta kora daga muhallansu wadanda yanzu haka ke rayuwa matsugunan wucin gadi.

Kungiyar ta Hamas ta ce akwai akalla mutane 150 da ta kame kuma kai tsaye za ta fara kashe su idan har Isra’ilan ba ta dakatar da luguden wuta kan al’ummar Gaza ba.

Zuwa yanzu alkaluman mutanen da suka mutu a bangaren Isra’ila ya tasamma dubu guda yayinda mutane 687 suka mutu a bangaren Falasdinu, kuma ake ci gaba da kaiwa juna farmaki, a harin wanda Isra’ila ta bayyana da makamancin harin Amurka na 9/11.

Cikin sanarwar da Hamas ta fitar dauke da sa hannun jagoranta, Ezzedine al-Qassam ta ce harin Isra’ila ya kashe 4 cikin mutanen da ta kama, kuma itama a shirye ta ke ta kammala kisan tarin Isra’ilawan da ke hannunta dama ‘yan kasashen ketare ciki har da Amurkawa kamar yadda shugaba Joe Biden ya yi ikirari.

Gargadin na Hamas na zuwa ne bayan wani jawabin Netanyahu da ke alakanta kungiyar da ISIS tare da shan alwashin murkushe yankin na Gaza, bayan da ta girke dakaru dubu 300 don yaki da mayakan wadanda ta kira da ‘yan ta’adda.

Anga dai yadda mayakan na Hamas su akalla dubu guda kamar yadda kungiyar ta yi ikirari, suka rufarwa Isra’ilan ta ruwa da kasa da kuma sararin samaniya a Asabar din da ta gabata.

Kakakin ma’aikatar tsaron Isra’ila Libby Weiss ta ce har yanzu Sojin kasar na gwabza fada da mayakan na Hamas a cikin Isra’ilan, yayinda ministan tsaro Yoav Gallant ke cewa za ku kamma yiwa Gaza kawanya don kange mutane miliyan 2 da dubu 300 da ke rayuwa a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.