Isa ga babban shafi

Isra'ila ta kashe Falasdinawa 198 bayan harin Hamas ya kashe 'yan kasar 70

Hare-haren Isra’ila sun hallaka Falasdinawa akalla 198, baya ga jikkata wasu dubu 1 da 610 a martinin da kasar ta mayar game da harin kungiyar Hamas wadda ta yi ruwan makaman roka da safiyar yau Asabar tare da kashe ‘yan Isra’ilan da bayanai ke cewa yawansu ya tasamma 70.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce kasarsa na yaki da kungiyar Hamas ne.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce kasarsa na yaki da kungiyar Hamas ne. AP - Ohad Zwigenberg
Talla

Hare-haren na Isra’ila, na zuwa ne bayan Firaminista Benjamin Netanyahu ya bayyana halin da ake ciki da yaki tsakanin kasar da yankin na Falasdinu.

Rahotanni sun bayyana cewa Isra’ila ta jibge tarin sojoji wadanda suka rika sauka a jiragen yaki tare da yin kan mai uwa da wani kan al’ummar ta yankin Gaza.

A cewar bayanai, mayakan na Hamas sun harba makaman roka fiye da dubu bakwai kan Isra'ila, wanda ke matsayin hari na baya-bayan nan da kungiyar ta kaddamar cikin tarin shekaru, wanda kuma tuni ta samu goyon bayan takwararta kungiyar Hezbollah ta Lebanon.

Mayakan Hamas a kan iyakar Isra'ila da yankin Gaza.
Mayakan Hamas a kan iyakar Isra'ila da yankin Gaza. AP - Hassan Eslaiah

Hare-haren na Isra’ila ga al’ummar Gaza ya samu cikakken goyon baya daga Amurka wadda ta ce kasar na da damar kare kanta daga hare-haren na mayakan Hamas.

Yanzu haka dai kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya na shirin gudanar da wani zaman gaggawa a gobe Lahadi don tattaunawa kan sabon rikicin na Isra’ila da Falasdinu.

Shugaba Joe Biden ya bayyana cewa zai tabbatar da ganin Majalisar ta bayar da cikakken goyon baya ga Isra’ila don kare al’ummarta ta kowanne hali.

Brazil wadda ke jagorancin karba-karba na kwamitin tsaro na Majalisar a wannan wata, ta yi tir da harin tare da bayyana shirin samar da mafita ga rikicin bangarorin biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.