Isa ga babban shafi

Hamas ta kashe wasu Falasdinawa saboda zargin hada kai da Isra'ila

Kungiyar ta Hamas ta masu kaifin kishin Islama, da ke mulki a zirin Gaza ta sanar da cewa ta zartar da hukuncin kisa kan Falasdinawa biyar, saboda zargin hada kai da Isra'ila.

Hamas dai na zargin mutanen da hada da dakarun Isra'ila
Hamas dai na zargin mutanen da hada da dakarun Isra'ila REUTERS/Stringer
Talla

 

Hukuncin shi ne na farko da aka aiwatar a yankin Falasdinawa fiye da shekaru biyar.

“An zartar da hukuncin kisa kan wasu mutane biyu da aka yi Allah wadai da su kan hada kai da Isra'ila, da kuma wasu mutum uku da aka samu da aikata manya laifuka,” in ji Hamas a cikin wata sanarwa.

Sanarwar ta kara da cewa, a baya an bai wa wadanda ake tuhuma “cikakken hakkinsu na kare kansu”.

Kungiyar Hamas ta yanke hukuncin kisa ga mutane da dama a cikin 'yan shekarun nan saboda "hada kai" da Isra'ila, amma hukuncin kisa da aka sanar shi ne na farko da aka aiwatar tun watan Mayun 2017.

An kashe mutanen ne a bainar jama'a, bayan samun su da laifin kisan wani babban jami’in sojin yankin.

An kama su ne makonni kadan da suka gabata kan kisan Mazen Faqha, wanda ake zargin an harbe shi a madadin Isra'ila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.