Isa ga babban shafi

Harin Isra'ila ya kashe Falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan

Mutane uku sun rasa rayukan su a yayin da sama da 30 suka gamu da munana raunuka a harin da Isra’ila ta kai yankin Nablus da ke yamma da Kogin Jordan.

Wannan na zuwa ne bayan kwanaki biyu da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta
Wannan na zuwa ne bayan kwanaki biyu da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta AP - Hatem Moussa
Talla

A cewar ma’aikatar lafiyar Palasdinu, harin na zuwa ne kwanaki biyu bayan kulla yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Ira’ila da Zirin Gaza, tare da bude Mashigin yankin daga Masar.

Kungiyar bada agaji ta Red Cresent reshen Palasdinu, tace ta karbi mutane 69 sakamakon Harbin bindiga don yi musu Magani, dukkan su daga Yankin Nablus, hudu daga cikin su kuma na cikin mawuyacin hali.

A sanarwar da Isra’ilan Yahudawa ta fitar, ta ce harin da ta kai ya hakkala wani dan ta’adda Ibrahim Al-Nabulsi da kuma wani na hannun damansa.

Ibrahim Nabulsi dai na cikin manyan kwamandojin Kungiyar dake gwagwarmayar kato masallaci Kudus, guda daga cikin kungiyoyi masu karfi da ke fafatawa da dakarun Isra’ila a yamma da kogin Jordan.

Haka kuma harin ya rutsa da wani yaro dan shekara 16, sai dai kuma Palasdinu tace matasan da suka mutu biyu ne har da wani dan shekaru 17, da aka harbe har lahira a kudancin birnin Hebron.

Kamfanin dillancin Labaran Faransa AFP ya ruwaito cewa a garin na Nablus anyi musayar wuta tsakanin Dakarun da ke gwagwarmayar kwatar ‘yancin Falasinu da kuma dakarun Isra’ila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.