Isa ga babban shafi

Kasashe sun fara mai da martani bayan harin Hamas ya kashe 'yan Isra'ila 70

Kasashen Duniya sun fara tofa albarkacin baki bayan hare-haren Hamas kan Isra’ila da zuwa yanzu suka kashe mutane 70 tare da jikkata wasu masu tarin yawa da safiyar yau Asabar kuma har zuwa yanzu ake ci gaba da gwabza fada tsakanin bangarorin biyu.

Falasdinawan kungiyar Hamas a Gaza yayin hare-harensu a Isra'ila.
Falasdinawan kungiyar Hamas a Gaza yayin hare-harensu a Isra'ila. AP - Hassan Eslaiah
Talla

Tuni Iran ta jinjinawa mayakan na Hamas yayinda jagoran Falasdinawa shugaba Mahmud Abbas ke cewa al’ummar yankin na Gaza na da damar kare kansu daga hare-haren da Isra’ila ke kai musu.

Kasashen Turkiya da Saudiya da kuma Rasha sun bunkaci sasantawa tsakanin bangarorin biyu don ci gaba da zaman lafiya yayinda shugaba Macron na Faransa ya bayyana hare-haren na Hamas da ta’addanci kan Isra’ila.

Sauran kasashen da suka tsoma baki a sabbin hare-haren na Hamas sun hada da Masar wadda ta yi gargadi kan yiwuwar tsanantar rikicin bangarorin biyu yayinda kungiyar tarayyar Turai ta yi tir da harin tare da bayyana kame mutanen da Hamas ta yi a matsayin abin da ya saba ka’ida.

Wani bangare na harin da mayakan Hamas suka kai a Gaza.
Wani bangare na harin da mayakan Hamas suka kai a Gaza. AP - Ohad Zwigenberg

Mayakan na Hamas sun yiwa Isra’ila ruwan dubban  makaman roka da safiyar yau Asabar wadanda suka harba ta kusan dukkanin sassa kama daga ruwa da kasa da kuma sararin samaniya.

Harin wanda ya zo a bazata, gomman mayakan na Hamas sun rarraba kansu, wajen yiwa jami’an tsaron kan iyakar Isra’ila dauki dai-dai, dai dai lokacin da kasar ke gudanar da bukukuwan al’adu.

Baya ga tarin mutanen da suka mutu da kuma wadanda suka jikkata, Hamas ta fitar da wani bidiyo inda ta ke nuna wasu ‘yan Isra’ila 3 da ta ce ta yi garkuwa da su, lamarin da ya tayar da hankalin duniya.

Har zuwa yanzu dai ana ci gaba da gwabza fadan na Hamas da Sojin Isra’ila yayinda kungiyar Hezbollah ta nuna cikakken goyon baya ga takwararta ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.