Falastinawan yankin Gaza sun kaddamar da hare haren Rokoki kan kasar Izraela
A yau assabar 7 ga watan Octoba, kungiyar gwagwarmaya da makamai ta Falestnawa ta harba wasu wasu Gwamman rokoki da daga yankin zirin Gaza zuwa cikin yankin da kasar Isarela ta kwace, al’amarin da ya kawo karshen tsagaita wutar da aka cimma tun bayan barkewar yakin kwanaki 5 da aka gwabza a cikin watan mayun da ya gabata.
Wallafawa ranar:
A cikin wata nadaddiyar murya da aka yada ta kafar TV din Al-Aqsa, ta kungiyar Hamas, komadan mayakan Ezzedine al-Qassam Mohammad Deif, ya bayyaa cewa, sun kaddamar da hare hare ne, domin kawo karshen mayamen da Isarela ke yi wa kasarsu, inda ya kara da cewa, a kalla sun harba rokoki sama da dubu 5000 tun da dugun dugun safiyar yau assaba, kawo lokacin rubuta rahoton. Ya kuma bukaci duk wani bafalastinen da ke da makami ajiye a gidansa da cewa, lokaci ya yi da ya kamata ya fito da shi ya yi aiki da shi.
Hare haren rokokin kan kasar Isareala dai, sun fara ne da misalin karfe 6 da mintina 30 na safiyar yau agogon can 6 Gaza 6 da minitina 30 a gogon GMT inda aka kwashe tsawo mintina 45 makamai na sauka babu kakkautawa.
A Isareala an jiyo tashin jiniyoyin fadakar da mutane a garuruwa da dama dake makwaftaka da yankin na falestinawa, haka kuma a birnin Jérusalem da kuma tsakkiyar yankunan arewa da yammacin kasar ta Isarela a cewar majiyar sojojin Yahudawa.
Yanzu haka dai dakarun na Izarai ;a sun faara mayar da martani abinda ake ganin zai maimaita abindaya saba faruwa a yaankin na malalar jinin babu kakkautawa
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu