Isa ga babban shafi

Harin Jenin: Kungiyar likitoci ta koka kan rashin samun damar isa wajen

Kungiyar likitocin kasa da kasa ta bukaci samun damar isa zuwa yankin Jenin na Falasdinu, don bada agaji ga marasa lafiyan da harin Isra’ila ya shafa ba tare da wata matsala ba. 

Yadda hayaki ya turnuke sararin subuhana, bayan harin da Isra’ila sansanin 'yan gudun hijira ta Jenin.
Yadda hayaki ya turnuke sararin subuhana, bayan harin da Isra’ila sansanin 'yan gudun hijira ta Jenin. © AFP / JAAFAR ASHTIYEH
Talla

Harin da Isra’ila ta kai kan sansanin 'yan gudun hijira shine mafi girma cikin shekaru 20 da suka gabata. 

Kungiyar likitocin ta ce marasa lafiyan da harin ya rutsa da su, na bukatar kulawar gaggawa, sai dai kuma akwai fargaba da kuma rashin tabbas ga jami’an ta wajen samun damar isa yankin. 

Bayan mutuwa da kuma jikkatar mutane, harin ya kuma lalata gine-ginen cibiyoyi lafiya da kuma shafar wasu jami’an kulada lafiya. 

Kungiyar ta kuma ce harin na Isra’ila ya lalata hanyoyin isa zuwa ga sansanin 'yan gudun hijirar Jenin din, abinda zai basu matukar wahala wajen isa don kaiwa marasa lafiya agajin gaggawa. 

Korafin na kungiyar likitocin na zuwa ne a dai-dai lokacin da liktoci da kuma jami’an lafiya na Falasinun suka fara tafiya a kafa don isa sansanin na Jenin, duk kuwa da hare-hare ta sama da kuma hare-harben bindiga da dakarun Isra’ila ke ci gaba da yi a yankin. 

Kawo yanzu dai adadin wadanda harin ya yi ajalin su ya kai 10, a cewar kafar yada labarai ta Al-Jazeera.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.