Mutane 9 sun mutu a hare-haren da dakarun Isra’ila suka kai yankin Falasdinu
Mutane 9 sun hallaka sakamakon hare-haren da dakarun Isra’ila suka kaddamar a wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke yankin Jenin na yamma da kogin Jordan.
Wallafawa ranar:
Kafin wannan hari, sai da dakarun na Isra’ila suka kashe wani matashi dan shekaru 21 mai suna Mohammed Hasanein a mashigin Ramallah da ke tsakiyar Faladinu, kamar yadda ma’aikatar lafiyar kasar ta tabbatar.
Mazauna yankin sun tabbatarwa manema labarai cewa Isra’ilan ta kai hare-hare kusan 10 kan yankin na Jenin cikin daren jiya Lahadi, lamarin da ya sanya hayaki turnuke sararin samaniya tare da rushe gine-gine.
Tun farko dai sojojin Isra’ilan sun zagaye sansanin 'yan gudun hijirar da tankokin yaki fiye da 10, kafin daga bisani suka fara luguden wuta lamarin da ya lalata gine-ginen da ke wajen.
Bayan ta fitar da jerin mutanen da suka mutu sanadin hare-haren, ma’aikatar lafiyar Palasdinu ta kuma ce fiye da Falasdinawa 30 ne suka gamu da munanan raunuka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu