Isa ga babban shafi

'Yan kasar Isra'ila sun yi zanga-zangar neman kawo karshen rikicin Falasdinawa

Dubun dubatar masu zanga-zanga ne suka fantsama titunan birane da garuruwa a fadin kasar Isra'ila a mako na 23, domin nuna adawa da shirin gwamnatin Firaminista Benjamin Netanyahu na yin garambawul a bangaren shari'a da kuma tsananta tashe-tashen hankula a yankin Falasdinawa.

Zanga-zangar adawa shirin garambawul ga fannin shari'a a Isra'ila   a Tel Aviv, 20 ga watan Mayu 2023.
Zanga-zangar adawa shirin garambawul ga fannin shari'a a Isra'ila a Tel Aviv, 20 ga watan Mayu 2023. AP - Tsafrir Abayov
Talla

 

Zanga-zangar da kusan mutane dubu 100 suka halarce ta ranar Asabar, ta fara ne tun cikin watan Janairu jim kadan bayan rantsar da gwamnatin Benjamin Netanyahu mai tsattsauran ra'ayi.

Ganin yadda masu zanga-zangar sama da 200,000 ke fitowa a wasu lokutan, masu shirya ta suka ce ba za su yi kasa a gwiwa ba har sai gwamnati ta soke sauye-sauyen a bangaren shari'a maimakon jinkirta shirin.

Tun daga farkon wannan shekarar, an kashe Falasdinawa da ‘yan Isra'ila kimanin 102 sakamakon tsanantan tashin hankalin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.