Isa ga babban shafi

Kasashe na ci gaba da maida martani kan rikicin da ake gwabzawa a Gaza

Kasashe da dama ne suka yi Allah wadai da hare-haren da Falasdinawa ke kaiwa ta kasa da ruwa da kuma ta sama cikin Isra’ila, wanda sojojinta suka ce kimanin mutane dubu daya suka mutu.

Wani bangare da Isra'ila ta kaiwa hari a zirin Gaza.
Wani bangare da Isra'ila ta kaiwa hari a zirin Gaza. AFP - MAHMUD HAMS
Talla

 

Tun bayan kaddamar da hare-haren da Hamas ta yi, wasu kasashen suka fara yin kira da a dakatar da rikicin, bayan da Isra'ila ta kaddamar da hare-hare martani ta sama a yankin zirin Gaza, wanda hukumomin Falasdinu suka ce sun yi sanadiyar mutuwar Falasdinawa fiye da 230.

Fara ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce kasar na cikin yaki, inda ya sha alwashin maida mummunan martani kan Hamas.

Kawo yanzu dai wasu kasashen duniya sun maida martini kan lamarin, inda shugaba Joe Biden na Amurka ya ce kasarsa za ta marawa Isira’ila baya, ta hanyar bata gudunmuwa.

Shugaba Joe Biden a lokacin da ya ke gabatar da jawabi gama da harin da aka kaiwa Isra'ila.
Shugaba Joe Biden a lokacin da ya ke gabatar da jawabi gama da harin da aka kaiwa Isra'ila. Getty Images via AFP - SAMUEL CORUM

A nata bangaren, kasar Iran goyon bayan hare-haren da Hamas ta kaddamar kan Isra’ila ta yi, inda ta ce za ta ci gaba da goya musu baya don samun ‘yancin Falasdinawa.Ita kuwa Majalisar Dinkin Duniya ta bakin shugabanta da ke kula da kare kakkin bil’adama Volker Turk, kira ya yi wa bangarorin biyu su kawo karshen rikicin.

Ya kuma nuna rashin jin dadinsa kan yadda aka yi garwa da wasu.

Kungiyar Tarayyar Turai ta bakin shugabanta Ursula von der Leyen, Allah wadai ta yi da harin na Hamas, inda ta ce Isra’ila na da hakkin kare kanta daga irin wadannan hare-hare.

Kasar Brazil da ke rike da shugabancin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, bukatar bangarorin ta yi su dakatar da rikcin don kaucewa yaduwarsa.

Sauran kasashe irinsu Saudiya da China da Rasha da Turkiya da Japan da kuma Afrika ta Kudu, bukaci dakatar da rikicin cikin gaggawa suka yi don kaucewa ci gaba da asarar rayuka.

 

Ya yinda a bangaren kasashen Faransa da Ukraine da Birtaniya da India da Jamus da kuma Venezuela, nuna goyon bayansu ga Isra’ila suka yi, inda suka ce ta na da hakkin maida martini don kare kanta.

Su kuwa ‘yan tawayen Huti da ke rike da Yemen, jinjinawa Hamas suka yi kan hare-haren ta kaiwa Isra’ila, wanda ta bayyana a matsayin kwato ‘yanci da kare kai.

Wata tankar yakin Isra'ila a kan babban hanyar Sderot.
Wata tankar yakin Isra'ila a kan babban hanyar Sderot. © AFP - RONALDO SCHEMIDT

Da sanyin safiyar Asabar din nan ne mayakan Hamas su ka yiwa Isra’ila ruwan dubban  makaman roka, wadanda suka harba ta kusan dukkanin sassa kama daga ruwa da kasa da kuma sararin samaniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.