Isa ga babban shafi

Hare-haren Isra'ila sun kashe mutane da dama a yankin Falasdinu

Rundunar sojin Isra’ila tace jiragen yakin ta sun yi ruwan bamai-bamai kan wasu wuraren kungiyar Hamaz a zirin Gaza, yayin da kungiyar ta ce an kashe manyan kwamandoji uku a hare-haren.

Wata yarinya a wani gini da Isra'ila da kai hare-hare ta sama a yankin Falasdinwa .09/05/23
Wata yarinya a wani gini da Isra'ila da kai hare-hare ta sama a yankin Falasdinwa .09/05/23 REUTERS - IBRAHEEM ABU MUSTAFA
Talla

Ma'aikatar lafiya ta Falasdinu ta ce an kashe mutane da dama tare da jikkatar wasu sakamakon hare-haren da Isra’ila ta sama.

Rundunar sojin Isra'ila ta ce an kai hare-haren ta sama ne kan gidajen wasu manyan kwamandojin kungiyar ta Hamaz da ke samun goyon bayan Iran.

Harin da jiragen yakin Isra'ila suka kai a zirin Gaza ya yi sanadiyar mutuwar shugabannin kungiyar Hamaz da wasu mutane 10 ciki harda kananan yara.

Daukar Fansa

Kungiyar Hamaz ta lashi takobin daukar fansa kan mutane da aka kashe a harin da aka kai da jiragen yakin Isra'ila kimanin 40 da safiyar wannan Talata.

Ma'aikatar lafiya ta Gaza ta ce yara hudu na daga cikin wadanda aka kashe, wasu 20 kuma suka jikkata, wasu daga cikinsu na cikin mawuyacin hali, a hare-haren da suka yi sanadiyyar kona gine-gine tare da mayar da wasu gine-ginen baraguzai.

Daga baya kuma, tashin hankali ya barke a yammacin gabar kogin Jordan da aka mamaye a lokacin da sojojin Isra'ila suka kaddamar da wani samame a Nablus inda akalla mutane goma suka samu raunuka, a cewar likitocin Falasdinu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.