Isa ga babban shafi

Isra'ila ta kame Falasdinawa 350 da ke Sallah Masallacin Qudus

'Yan sandan Isra’ila sun kame Falasdinawa fiye da 350 a wani sumame da suka kai cikin Masallacin Al-Aqsa lokacin da musulmi ke tsaka da sallah, lamarin da ya juye zuwa rikici tsakanin bangarorin biyu.

Falasdinawa yayin rikici da 'yan sandan Isra'ila a masallacin al-Aqsa na birnin Qudus.
Falasdinawa yayin rikici da 'yan sandan Isra'ila a masallacin al-Aqsa na birnin Qudus. AFP - AHMAD GHARABLI
Talla

Rahotanni sun ce jami’an ‘yan sandan na Isra’ila sun yi yunkurin tarwatsa masu Sallar ne bisa kafa hujja da cewa sun dade a cikin masallacin fiye da wa’adin da aka dibar musu, lamarin da ya sanya falasdinawa tirjiya don bayar da kariya ga masallatan.

Bayan kamen da kuma jikkata wasu da dama a rikicin da daren jiya talata kari kan  hari da jiragen Soji da Isra’ila ta kai kan zirin Gaza, kungiyar Hamas da ke jagorancin yankin ta mayar da martani ta hanyar farmakar Isra’ila da wasu makamai masu linzami.

Rikicin bangarorin biyu bayan mamaye gabashin birnin Qudus da Isra’ila na kara zafafa ne a dai dai lokacin da al’ummar musulmi ke azumin watan Ramadana wanda a wannan karon ya zo dai dai da wani bikin al’ada na Yahudawa.

Tun farko Hamas ta bukaci al’ummar yankin da su fita su kare masallacin daga Yahudawan kama guri zauna, lamarin da ya kai ga rikicin tare da kamen tarin mutanen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.