Isa ga babban shafi

Isra'ila ta kashe Falasdinawa 10 yayin sumame a yammacin kogin Jordan

Sojojin Isra’ila sun kashe Falasdinawa 10 a wani samame da suka kai musu a yankin Yamma ga Kogin Jordan a jiya Alhamis 

Harin shi ne na baya-bayan nan da Isra'ila ta kai kan Falasdinawa.
Harin shi ne na baya-bayan nan da Isra'ila ta kai kan Falasdinawa. © MAHMUD HAMS/AFP
Talla

Sojojin na Isra’ila sun bayyana samamen a matsayin wani aikin kakkabe ‘yan ta’adda, kuma wannan kisan shi ne mafi muni da aka gani cikin shekaru masu yawa a yankin na Yamma ga Kogin Jordan. 

An kaddamar da samamen ne kan dandazon ‘yan gudun hijira sansaninsu a birnin Jenin da ke yankin, inda aka yi ta jin karar harbe-harben bindiga a unguwanni, sannan hayaki ya turnuke sararin samaniya saboda konewar wasu shingaye. 

Ministan Lafiyar Falasdinu ya ce, baya ga mutanen 10 da suka kwanta dama, har ila yau akwai wasu 20 da suka samu raaunuka. 

Tun lokacin da ta fara tattara alkaluman kisa a yankin Yamma ga Kogin Jordan a shekarar 2005, Majalisar Dinkin Duniya ba ta taba samun alkaluman kisa masu yawa a sanadiyar wani samame na rana guda ba  kamar wannan da aka yi a jiya Alhamis. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.