Isa ga babban shafi

Biden ya gargadi Isra'ila kan maimaita irin kuskuren da Amurka ta yi a baya

Shugaba Joe Biden, ya gargadi Isra’ila kada ta maimaita irin kuskuren da Amurka ta yi bayan harin ta’addanci na 11 ga watan Satumba, a daidai lokacin da sojojin Isra'ila ke shirin kai farmaki ta kasa, a matsayin martani ga hare-haren da Hamas ta kai ma ta wadanda suka yi sanadiyar mutane sama da dubu daya. 

Shugaban Amurka Joe Biden yayin ganawa da Faranministan Isra'ila Benyamin Netanyahu a Tel Aviv .18/10/23
Shugaban Amurka Joe Biden yayin ganawa da Faranministan Isra'ila Benyamin Netanyahu a Tel Aviv .18/10/23 © EVELYN HOCKSTEIN/REUTERS
Talla

A jawabin da shugaba Biden ya gabatar a babban birnin kasar Tel Aviv, bayan kamala ziyarar wuni guda da ya kai Isra’ila a wannan Laraba, ya ce mayar da martani cikin fushi na da illa, amma dai ya kamata Isra’ila ta shirya manufar da take son cimmawa a hare-harenta.

Ina kira da kuyi taka tsantsan yayin da kuke jin cewa ba zaku iya hadiye fushin ku ba, bayan harin ranar 9 11, mun fusata yayin da muke neman adalci, mun kuma tafka kurakurai. Ni ne shugaban Amurka na farko da ya ziyarci Isra'ila a lokacin wannan yaki, na dauki matakai da dama a lokacin yaki, na sani ba abu bane mai sauki ga shugabanni, akwai bukatar fayyace manufofin da ake son cimmawa ko hanyar da za a bi don cimma wadannan manufofin. Mafi yawan Falasdinawa ba ‘yan Hamas ba ne. Hamas ba ta wakiltar al'ummar Falasdinu.  

Shugaban na Amurka ya ce yana goyon bayan samar da mafita kan rikicin Faladinawa da Isra’ila, musamman ta hanyar samar da kasashe biyu masu cin gashin kansu. 

A gare ni, ina goyon bayan manufar samar da kasashe biyu don samar da hadin gwiwar Isra'ila da makwabtanta. Wadannan hare-haren sun kara karfafa himma da azama da kuma niyyata na yin hakan. Ina nan ne don shaida muku cewa 'yan ta'adda ba za su yi nasara ba, cin gashin kai ne zayyi nasara. 

Biden dai shine shugaban wata kasa na farko da ya ziyarci Isra’ila, tun bayan fara rikici tsakanin Hamas da ita a ranar 7 ga wannan wata na Oktoba.  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.