Isa ga babban shafi

Dubban mutane sun yi zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a Amurka

Dubban mutane sun gudanar da zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a birnin Washington DC, inda suka dangana da fadar gwamnatin Amurka ta White House a jiya Asabar yayin da suke rera waken neman ‘yan cin yankin Falasdinu.

Masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a gaban fadar gwamnatin Amurka ta White House.
Masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a gaban fadar gwamnatin Amurka ta White House. © ANDREW CABALLERO-REYNOLDS / AFP
Talla

Hotunan bidiyon da suka yadu, sun nuna cewar baya ga gangamin magoya bayan Falasdinawa, masu marawa Isra’ila baya sun gudanar da nasu tattakin a tsawon mako gudan da aka shafe Isra’ilar na kai farmaki ta sama kan Zirin Gaza, yayin da mayakan Hamas ke maida mata martani da makaman roka.

Tun a farkon makon da ya kare dubun dubatar mutane ke jerin gwanon yin Allah wadai da hare-haren Isra'ila kan Zirin Gaza, inda rayukan fararen hular da suke salwanta ke karuwa, yayin da a wasu kasashen magoya bayan Isra'ila ke gangamin mara mata baya, kan matakin kare kanta da suka ce tana da 'yancin dauka.

A baya bayan nan ne dai kungiyoyin agaji suka yi gargadin cewa gudun hijirar tilas ya sake tsananta mayuwacin halin da dubun dubatar Falasdinawa ke ciki a yankin Gaza da Isra’ila ta yi wa kawanya.

Har yanzu dai dubban mutane na ci gaba da  kokarin ficewa daga arewacin Zirin Gaza, bayan da Isra’ila ta baiwa Falasdinawa sama da miliyan daya umarnin komawa kudancin yankin, kafin ta kaddamar da farmaki da sojojin kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.