Isa ga babban shafi

Sabon farmakin Isra'ila ya hallaka sama da mutum 40 a kudancin Gaza

Sama da mutane 40 ne suka mutu sannan wasu akalla 21 suka jikkata a wani hari da jiragen yakin Isra'ila suka kai a kudancin zirin Gaza cikin dare, yayin da wani babban jami’in gwamnatin Amurka ya sanar da murabus din sa saboda taimakon da Washintan ke bai wa Isara’ila.

Wasu masu zanga-zangar goyan bayan Falasdinu. 18/10/23
Wasu masu zanga-zangar goyan bayan Falasdinu. 18/10/23 AFP - FETHI BELAID
Talla

Kamfanin dillancin labaran Falasdinawa ya ruwaito cewar, sabbin hare-haren da Isra’ila ta kaddamar cikin dare, an kai su ne kan rukunin gidajen wasu iyalai uku a birnin Rafah dake kuduncin zirin Gaza.

Har ila yau, jiragen saman Isara’ila sun kai hari kan wata  hasumiyar al-Masry da ke Rafah din.

Mashigar Rafah na yankin Gaza ta kan iyaka da Masar.
Mashigar Rafah na yankin Gaza ta kan iyaka da Masar. © IBRAHEEM ABU MUSTAFA / REUTERS

Sojojin gwamnatin Isra'ila sun kai farmaki kan wasu yankuna a yammacin gabar kogin Jordan da suka mamaye, inda suka kashe mutane da dama ciki har da matasa biyu tare da kame wasu da ake zargin 'yan kungiyar Hamas ne.

Shigar da kayan agaji Gaza

Shugaba Biden ya ce ya samu nasarar ƙulla wata yarjejeniya da za ta bayar da damar kai agaji Gaza, kwanaki  bayan da Isra’ila ta kaddamar da luguden wuta da ya jefa jama’a cikin bukatar tallafi.

Shugaban kasar Amurka Joe Biden yayin ziyara a Isra'ila. 18/10/23
Shugaban kasar Amurka Joe Biden yayin ziyara a Isra'ila. 18/10/23 via REUTERS - POOL

Mista Biden ya bayyana hakan ne a kan hanyar sa ta komawa Amurka bayan gajerar ziyrar da ya kai Isra’ila, inda ya ce shugaba Abdel Fattah el-Sisi ya amince da bude mashigar Rafah don shigar da manyan motoci 20 dauke da kayan agaji zuwa Gaza.

Shugaban kasar Masar Abdel Fattah El-Sisi ya tabbatar da  bada damar tsallakawa da kayan agaji zuwa zirin Gaza ta mashigar Rafah, yayin da daruruwan motocin agaji ke jira a mashigar yankin da Isra'ila ke ci gaba da kai wa hari.

China na neman kawo karshen rikicinShugaban kasar China Xi Jinping ya shaidawa firaministan Masar Mostafa Madbouly cewa, Beijing na son yin aiki tare da Masar don samar da kwanciyar hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.

Rasha ta fara tura kayan agaji

Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta ce za ta kai tan 27 na kayan agaji, galibi kayan abinci, ga mutanen da suka makale a zirin Gaza.

Motoci dauke da kayan agaji a Rafah
Motoci dauke da kayan agaji a Rafah REUTERS - STRINGER

Wani jirgin sama dauke da kayan yana kan hanyarsa ta zuwa Arish, wani birni na Masar a arewacin Sinai wanda ke da tazarar kilomita 50 daga kan iyakar Rafah.

Sannan ana sa ran kungiyar agaji ta Red Crescent ta Masar za ta tabbatar da cewa za a kai agajin, in ji ma'aikatar.

An kashe sama da Falasdiwa 3,480

Tun bayan barkewar sabon rikicin kusan Falasdinawa 3,480 ne aka tabbatar da mutuwarsu a hare-haren da Isra’ila ta kai a Gaza, amma adadin bai kunshi sama da 40 da aka kashe cikin daren Laraba ba, yayin da harin da Hamas ta kai cikin Isra'ila kuwa ya kashe mutane fiye da 1,400.

Wata 'Yar Falasdin da harin Isra'ila ya rutsa da su a yankin Gaza. 17/10/23
Wata 'Yar Falasdin da harin Isra'ila ya rutsa da su a yankin Gaza. 17/10/23 © AP / Abed Khaled

 

Murabus din babban jami'in Amurka

A halin da ake ciki, wani babban jami'i a ma'aikatar harkokin wajen Amurka ya sanar da murabus din sa kan abin da ya bayyana a matsayin rashin amincewarsa game da ci gaba da taimakawa Isra'ila, ta na kashe bayin Allah.

Josh Paul, wanda darakta ne a harkokin siyasa da soji na ma'aikatar harkokin wajen Amurka, ta shafinsa n asada zumunta, ya bayyana fargabar mamaita abin da aka yi a baya.

“Ina tsoron kada mu maimaita irin kura-kuran da muka tafka a shekarun baya-bayan, kuma in kasance a bangaren wannan alhaki na tsawon lokaci."

Paul, wanda ke aiki a bangaren musayar makamai na Amurka, ya ce ba zai iya "aiki ba don kara bai wa Isra’ila karin makamai.  

 

Shugaban Amurka Joe Biden tare da Franministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a Tel Aviv. 18/10/23
Shugaban Amurka Joe Biden tare da Franministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a Tel Aviv. 18/10/23 via REUTERS - POOL

 

Ya ce Amurka ta yi kaurin suna wajen nunawa kasashe yatsa kan take hakkin bil’adama, amma kuma ta kau da kai Isra’ila na wuce gona da iri.

Amurka ta na bai wa Isra'ila tallafin soja na sama da dala biliyan 3.8 a duk shekara.

Ziyarar Franministan Birtaniya

Faranministan Birtaniya Rishi Sunak ya sauka a birnin Tel Aviv  a wata ziyarar nuna goyon baya ga Isra'ila.

Mista Sunak zai mika sakon ta'aziyya ga takwaransa na Isra'ila, Benjamin Netanyahu, dangane da harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba, tare da tattauna kan rikicin na yakin Gaza.

 

Faranministan Burtaniya Rishi Sunak yayin ganawa da sarkin Jordan.15/10/23
Faranministan Burtaniya Rishi Sunak yayin ganawa da sarkin Jordan.15/10/23 © HANNAH MCKAY / Reuters

 

A yayin ziyarar ta kwanaki biyu a yankin, ana sa ran Sunak zai ziyarci Masar da kuma kasar Qatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.