Isa ga babban shafi

Amurka na shan caccaka kan hawa kujerar naki a game da tsagaita wuta a Gaza

Amurka ta sake hawa kujerar naki a kan kudirin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a game da batun tsagaita wuta a yakin da Israila ke yi a Gaza, lamarin da ya haddasa caccaka daga abokan hamayyarta da ma abokanta.

 Amurka na shan caccaka kan hawa kujerar naki a game da tsagaita wuta a Gaza.
Amurka na shan caccaka kan hawa kujerar naki a game da tsagaita wuta a Gaza. AP - Mohammed Dahman
Talla

Karo na 3 kenan Amurka ke hawa kujerar naki a game da kudirin kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a game tsagaita wuta a Gaza, kuma yana zuwa kwana guda bayan da Amurka ta sanar da cewa za ta goyi bayan tsagaita wuta na wucin gadi idan za a saki wadanda ake garkuwa da su a Gaza.

Kuri’ar da kwamitin mai mambobi 15 ya kada ya nuna cewa kasashe 13 na goyon bayan tsagaita wuta, 1, wato Amurka ke goyon bayan akasin haka, a yayin da Birtaniya ta bijire wa kada kuri’a.

Zaman taron Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.
Zaman taron Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya. AP - Seth Wenig

Wannan na nuni da yadda kasashen duniya da dama ke bukatar a dakatar da yakin Gaza, wanda ya  yi sanadin mutuwar Falasdinawa sama da dubu 29.

Ga yadda kasashen duniya suka mayar da martani:

China

Zhang Jun, jakadan China a Majalisar Dinkin Duniyaa ya bayyana takaicinsa da rashin gamsuwa da rashin gamsuwa da matakin Amurka. Kamar yadda kamfanin dillancin labaran China,  Xinhua  ya ruwaito.

Ya kara da cewa, “hawa kujerar naki da Amurka ta yi ya aike da sako mara armashi, lamarin da ya jefa halin da ake ciki a Gaza cikin karin hatsari. Matakkin Amurka tamkar bada damar ci gaba da kisa ne”.

Rasha

Jakadan Rashaa a Majalisar Dinkin Duniya, Vasily Nebenzia ya ce “hawa  kujerar naki da Amurka ta  yin a alamta wani bakin babi a tarihin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya”.

Ya zargi Amurka da koakrin bai wa Isra’ila isasshen lokaci na kammala shirinta na korar Falasdinawa a yankinsu.

Faransa

Jakadan Faransa a Majalisar Dinkin Duniya, Nicolas de Riviere ya bayyana takaici a kan matakin Amurka, duk da mummunan halin da ake ciki a Gaza.

De Riviere ya kara da cewa  Faransa  ta zabi a tsagaita wuta  a yayin kada kuri’a, kuma za ta ci gaba da aikin ganin an kubutar da wadanda ake garkuwa da su.

Rafah, birinin da Isra'ila ke kokarin kutsawa da dakarunta a bayaa bayan nan.
Rafah, birinin da Isra'ila ke kokarin kutsawa da dakarunta a bayaa bayan nan. AFP - SAID KHATIB

 

Algeria

Jakadan Algeria Majalisar Dinkin Duniya ya ce “an sake gazawa wajen cimma tsagaita wuta” kana ya yi kashedi a gamme da irin tasirrin da hakan zai yi a yankin Gabas ta Tsakiya baki daya.

Hamas

Hamas ta fitar da wataa sanarwar da ke cewa, matakin gwamnatin Joe Biden na hawa kujerar naki a kan kudirin tsagaita wuta goyon baya ne ga kudirin Isra’ila na ci gaba da mamayar yankin Falasdinawa da kisan Falasdinawa tare da daidata su.

Mahukuntan Falasdinawa

Ofishin shugaban Falasdinawa, Mahmoud Abbas ya ce hawa kujerar naaki da Amurka ta yi a wannan lokaci tamkar bai wa Isra’ila damar ci gaba da mamaya a yaanunan Falasdinawa ne, da kuma kaddamar da mummunan hari a kan birnin Rafah.

Qatar

Jakadar Qatar a Majalisar Dinkin Duniya,  Alya Ahmed Saif Al Thani  ta ce ta ji taakaicin gaza karbar kudirin tsagaaita wuta a Gaza sakaamakon kujerar naki da Amurka ta hau, sannan ta sha alwashin ci gaba da aikin ganin an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.

Saudi Arabia

Ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya ta ce abin takaici ne ya  faru a Kwamitinn Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, inda ta jaddadabukatar sake fasalin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.

 

 

Shugabar Amnesty Agnes Callamard.
Shugabar Amnesty Agnes Callamard. AP - Christophe Ena

 

Amnesty International

Agnes Callamard, shugabar kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty ta ce “Amurka na da damar kare fararen hula Falasdinawa, amma ta zabi ta yi akasin haka”.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.