Isa ga babban shafi
YAKIN GAZA

Amurka ta ki amincewa da shirin tsagaita wutar da Aljeriya ta gabatar

Duniya – Amurka ta hau kujerar naki wajen kin amincewa da kudirin da kasar Algeriya ta gabatar domin kiran tsagaita wuta a yakin Gaza lokacin da kwamitin sulhu na Majalisar dinkin duniya ya yi zama na musamman a yau.

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya  Linda Thomas-Greenfield
Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Linda Thomas-Greenfield REUTERS - MIKE SEGAR
Talla

Bayan tafka mahawara, kasashe 13 daga cikin 15 sun goyi bayan kudirin tsagaita wutar, yayin da Amurka ta ki amincewa da shi, sai kuma Birtaniya da taki kada kuri’ar ta.

Wannan ya kawo karshen hasashen da ake da shi na samun amincewar kwamitin sulhun wajen ganin an amince da bukatar tsagaita wuta domin dakatar da yakin da yanzu haka ya hallaka Falasdinawa sama da dubu 29.

Yayin da take jawabi bayan kayar da kudirin, Jakadiyar Amurka a Majalisar Linda Thomas-Greenfield tace rashin hankali ne ci gaba da akayi wajen kada kuri’ar neman tsagaita wutar, domin su ba zasu goyin bayan matakin ba, ganin yana iya haifar da tarnaki a tattaunawar da ake yi domin ganin an saki mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su.

Thomas-Greenfield tace Amurka zata gabatar da wani daftari na daban nan gaba kadan wanda ya sha banban da wadda kasar Algeriyar ta gabatar domin mahawara a kai da kuma amincewa da shi.

Jakadiyar tace shirin na Amurka zai kuma bada damar isar da kayan agaji ga Falasdinawa fararen hula mabukata, yayin da ta bayyana cewar Amurka a shirye take ta ci gaba da tattaunawa da wakilan kwamitin sulhun da kuma bangarorin dake shiga tsakani domin samun biyan bukata.

Wannan shine karo na uku da Amurka ke hawa kujerar naki wajen mahawarar tsagaita wutar a yakin Gaza da yanzu haka ya wuce watanni 4.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.