Isa ga babban shafi

Masar na aikin kebe wani yanki a iyakar Gaza don tsugunar da Falasdinawa

Masar ta ware wani yanki a kan iyakarta da Gaza don mayar da shi tudun mun tsira a wani shirin ko ta kwana kan hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kaiwa birnin Rafah, mafi girma da ke hannun kungiyar Hamas, wanda kuma ke matsayin matsuguni ga Falasdinawa fiye da miliyan 1 da dubu 400 da Isra’ilar ta tilastawa barin matsugunansu.

A convoy drives by at the Israel-Gaza border, amid the ongoing conflict between Israel and the Palestinian Islamist group Hamas, in Israel, January 25, 2024.
Wani ayain motocci a iyakar Isra'ila da Gaza. REUTERS - AMIR COHEN
Talla

A wani shirin ko ta kwana da Masar ke yi don tunkarar yakin na Isra’ila a Gaza, wasu majiyoyi sun tabbatar wa manema labarai yadda kasar ta ware yankin mai matukar girma, wanda aka yi kiyasin zai iya samar da wajen zama ga dukkanin Falasdinawan da Isra’ila ke ci gaba da kora daga yankunansu a cewar wasu majiyoyi.

Majiyoyin sun ce Masar ta dauki matakin ne lura da yadda kiraye-kiraye suka gaza tasiri wajen hana Isra’ilan ci gaba da hare-harenta a birnin Rafah dai dai lokacin da Falasdinawn da Isra’ilan ta kashe ke kai dubu 29 da ‘yan doriya.

Sai dai tuni Masar ta musanta wannan batu tare nanata gargadinta na cewa hare-haren na Isra’ila zai iya tilasta Falasdinawan kwararawa zuwa Sinai batun da ta ce babu wanda zai lamunci faruwarsa, musamman yadda kasashen Larabawa musamman Jordan ke ci gaba da gargadi kan faruwarsa.

Amurka dai ta jima ta na gargadin cewa ba za ta yarda da duk wani yunkurin kwashe Falasdinawan zuwa wani yanki a wajen Gaza ba.

Sai dai majiyoyin da ke tabbatar da labarin sun ce Masar na ci gaba da gyaran yankin wanda ke cikin sahara inda ta sanya dukkanin kayakin bukata don bayar da matsuguni ga Falasdinawan na yankin Gaza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.