Isa ga babban shafi

Ambaliyar ruwa ta mamaye titunan Daular Larabawa, Oman da kuma Bahrain

Saukar ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ɗauke da iska mai ƙarfi, da suka haddasa ambaliyar ruwa a sassan kasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, ya tilasta wa babban filin jiragen saman birnin Dubai karkatar da jirage da dama da a baya aka tsara za su sauka a birnin.

'Yadda ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ya haddasa ambaliyar ruwa a sassan Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa. 17 ga Afrilu, 2024.'Yadda ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ya haddasa ambaliyar ruwa a sassan Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa. 17 ga Afrilu, 2024.
'Yadda ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ya haddasa ambaliyar ruwa a sassan Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa. 17 ga Afrilu, 2024.'Yadda ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ya haddasa ambaliyar ruwa a sassan Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa. 17 ga Afrilu, 2024. AP - Jon Gambrell
Talla

Ruwan saman mai ƙarfi, ya kuma haddasa ambaliyar ruwan a sassan Bahrain da kuma ƙasar Oman, inda rayukan mutane 18 suka salwanta a tsakanin ranakun Lahadi zuwa Litinin da suka gabata.

A birnin Dubai, ruwan saman mai ɗauke da iska mai ƙarfi ya tilasta dakatar da sauka da tashin jiragen sama na tsawon mintuna aƙalla 25, kafin lamurra su daidaita.

Daya daga cikin titunan kasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da ambaliyar ruwa ta mamaye.
Daya daga cikin titunan kasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da ambaliyar ruwa ta mamaye. © AP

Bayanai sun ce jiragen da ke neman tashi daga katafaren filin nasu da ke birnin na Dubai ne kaɗai suka riƙa zirga-zirga da yammacin jiya, suma ɗin sai da suka riƙa fuskantar tsaiko saboda yadda motoci ba sa iya ratsa hanyoyin da ke kai wa da filin jiragen, biyo bayan ambaliyar ruwan da ta mamaye su.

A ƙasar Oman kuwa, ambaliyar ruwan rayukan mutane 18 ta lakume, cikinsu kuma har da wasu kananan yara ‘yan makaranta da wasu manya uku, bayan da ambaliyar ta yi awon gaba da motar da suke ciki a ranar Lahadin da ta  gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.