Isa ga babban shafi

Wadanda suka tsira daga ambaliyar Libya sun dukufa wajen laluben ‘yan uwansu

Wadanda suka tsira daga ambaliyar ruwan da ta afka wa sassan Libya musamman a birnin Derna da ke tsakiyar kasar, sun ci gaba da laluben baraguzan gine-gine da suka rushe cike da fatan gano ‘yan uwansu da suka bace, wadanda aka cire tsammanin samunsu da rai.

Daya daga cikin 'yan Libya a birnin Derna, da suka dukufa wajen neman 'yan uwansu da suka bace a iftila'in ambaliyar ruwan da ake fargabar ta kashe mutane sama da dubu 10 a kasar.
Daya daga cikin 'yan Libya a birnin Derna, da suka dukufa wajen neman 'yan uwansu da suka bace a iftila'in ambaliyar ruwan da ake fargabar ta kashe mutane sama da dubu 10 a kasar. AP - Yousef Murad
Talla

Wannan na zuwa ne yayin da mahukunta a kasar ta Libya ke fargabar barkewar cutuka masu yaduwa a sassan da iftila’in ambaliyar ya afka wa, saboda yawaitar gawarwakin da ka iya rubewa kafin a kai ga suturta su.

A ranar Lahadin da ta gabata, guguwa mai karfin gaske dauke da ruwan sama kamar da bakin kwarya, ta yi sanadin fashewar wasu manyan madatsun ruwa guda biyu, tare da haddasa tumbatsar kogin da ya ratsa tsakiyar birnin na Derna, lamarin da yayi sanadin shafe manyan gine-ginen benaye zuwa cikin teku, a daidai lokacin da dubban iyalai ke tsaka da barci.

Dukkanin allkaluman da suka banbanta da hukumomi ke bayar wa dangane da adadin mutanen da suka mutu sakamakon bala’in ambaliyar ruwan na Libya, na tabbbatar da cewa dubban rayuka aka rasa, yayin da magajin garin Derna, Abdulmenam al-Ghaithi, ya ce yawan wadanda suka rasa rayukan na su a birnin kadai ka iya kai wa mutane dubu 18 zuwa dubu 20.

Tuni dai tawagar masu aikin ceto daga kasashen Masar, da Tunisia, da Hadaddiyar Daular Larabawa, da Turkiya da kuma Qatar suka isa kasar ta Libya domin karfafa ayyukan jin kai da ke gudana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.