Isa ga babban shafi

Kotun tsarin mulkin Mali ta yi watsi da bukatar jam'iyyun siyasa

A kasar Mali, kotun tsarin mulkin kasar ta ayyana kanta a matsayin wacce a hukumance  ba za ta iya soke ko kawo gyara ga matakin da gwamnatin mulkin sojan kasar Mali ta dauka na dakatar da ayyukan jam'iyyoyin siyasar wannan kasa.

Alkalan kotun kolin kasar Mali
Alkalan kotun kolin kasar Mali © Annie
Talla

Da daukar wannan mataki daga majalisar sojin kasar ne wasu daga cikin wakilan kungiyoyin farraren hula  akasar ta Mali suka ruga kotun tare da bukatar ganin ta soke wannan mataki,said ai a yau Asabar,kamfanin dillancin labaren Faransa na AFP ya ruwaito cewa kotun tsarin mulkin wannan kasa ta nisanta kan ta daga  hukumar da za ta iya dannawa gwamnati burki a wannan yunkuri nata.

Dakarun kasar Mali
Dakarun kasar Mali © OLYMPIA DE MAISMONT / AFP

Majalisar sojin kasar ta Mali karkashin Shugabancin Kanal Assimi Goita  da ya karbi mulki bayan juyin mulki a shekarar 2020,ya aiwatar da sauye-sauye tsawon lokaci,da ake kyautata zaton sun shafi bangaren tsaron kasar na Mali.Wasu bayyanan sirri na bayana cewa ana zargin wadanan jam’iyyun siyasa da kokarin hargitsa lamuran tsaro da kuma kawo rudani a wannan lokaci da kasar ta Mali ke kokarin dawo sahun kasashe masu tsaro a Africa.

Taron goyon bayan majalisar sojin kasar Mali
Taron goyon bayan majalisar sojin kasar Mali © AP

Sai dai jam’iyyun siyasa da kungiyoyi na yiwa sojojin kalon wandada suka sabawa alkawarin da suka da una mika mulki  a ranar 26 ga watan Maris, 2024, alkawarin da suka dau gaban kasashen Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.