Isa ga babban shafi

Wasu da aka yi garkuwa dasu makon da ya gabata a Mali sun shaki iskar 'yanci

‘Yan ta’addan da ke ikirarin Jihadi a Mali sun saki mutane sama da 100 da suka sace a ranar Talatar da ta gabata a motocin bas guda uku da suke tafiya tsakanin garin Bandiagara zuwa Bankass na tsakiyar kasar.

Taswirar kasar Mali
Taswirar kasar Mali © Studio FMM
Talla

Kafafen yada labarai na kasar sun bayyana cewa, ‘yan ta’addan Katiba Macina da ke Ikirarin Jihadi dake karkashin Kungiyar Al-Qaeda ne suka sace mutanen, yayin da har yanzu akwai wasu mutanen da suka yi garkuwa da su kuma basu sake su ba.

Da yawa daga cikin wadanda ‘yan tawayen suka yi garkuwa da su a ranar 16 ga watan nan na Afirilu da muke ciki sun hada da mata da yara ne, inda yawancin su mazauna kauyukan da ke kusa da wurin ne.

Duk da yake har yanzu dai akwai wasu adadin mutane da dama da ‘yan ta’addan basu saka ba amma har yanzu ba takamamman adadinsu a hukumance duba da a ranar kasuwa ce aka yi garkuwa da su.

Kawo yanzu dai babu wata kungiyar da ta dauki alhakin wannan ta’addanci, sai dai mutanen da RFI ya tuntuba a yankin da suka nemi a sakaya sunan su, sun bayyana cewa ‘yan kungiyar Katiba Macina na Jnim ne suka aikata wannan aika-aika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.