Isa ga babban shafi

Amurka za ta mayar da sansanin sojinta zuwa Ivory Coast

Wani rahoton da fitacciyar Jaridar nan ta Juene Afrique ta wallafa a karshen watan Afrilu, ya bayyana cewar Amurka ta fara tuntuɓar gwamnatin Ivory Coast don buɗe sansanin sojinta a ƙasar.

Daya daga cikin dakarun Amurka na musamman dake horar da dakarun sojin Jamhuriyar Nijar a yankin Diffa. 4/Maris/2014.
Daya daga cikin dakarun Amurka na musamman dake horar da dakarun sojin Jamhuriyar Nijar a yankin Diffa. 4/Maris/2014. REUTERS/Joe Penney/File photo
Talla

Rahoton ya ce, shugaban rundunar  sojin Amurka da ke kula da nahiyar Afrika wato AFRICOM, Michael Langley ne ya mika buƙatar ga shugaba Alassan Ouattara, yayin ziyarar da ya kai masa tsakanin ranakun 28 da 29 na watan Afrilun da ya gabata.

A halin yanzu dai Amurka ta rasa tudun dafawa ta fuskar soji a yankin Sahel tun bayan da sojojin Nijar suka bukaci ficewar dakarunta daga kasar, yayin da makomar sojojin da ta girke a Chadi kuma ta kasance cikin halin rashin tabbas.

A farkon watan Janairu ne, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinke ya kai ziyara kasashen Ivory Coast, Cape verde da kuma Najeriya, inda ya bayyana cewa kasarsa za ta ware dala miliyan 45 domin samar da kwanciyar hankali a yammacin Afirka.

A cewar Jaridar, gwamnatin Amurka za ta samar da dala miliyan 65 a shekarar 2024 kadai, domin yakar ayyukan ta'addanci da tabbatar da tsaron iyakar Ivory Coast da ta rabata da burkina Faso mai fama da tashe-tashen hankulan maasu dauke da makamai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.