Isa ga babban shafi

Amurka ta amince za ta janye sojojinta da ke Jamhuriyar Nijar

Amurka ta amince ta janye sojojinta fiye da 1,000 dake Jamhuriyar Nijar, inda take da wani babban sansanin jiragen yaki mara matuki a yammacin Afirka, kamar yadda jami'ai suka bayyana.

Tutotin Amurka da Nijar kafada da kafada a sansanin sojojin sama da kuma sauran jami'an da ke goyon bayan gina sansanin sojin saman Niger Air Base 201 a Agadez, Nijar, Afrilu 16, 2018.
Tutotin Amurka da Nijar kafada da kafada a sansanin sojojin sama da kuma sauran jami'an da ke goyon bayan gina sansanin sojin saman Niger Air Base 201 a Agadez, Nijar, Afrilu 16, 2018. AP - Carley Petesch
Talla

Mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka Kurt Campbell ya tabbatar da matakin yiyin wata ganawa da ya yi da firaministan Nijar Ali Mahaman Lamine Zeine a birnin Washington, kamar yadda wasu jami'an Amurka da suka nemi a sakaya sunansu suka shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP.

Tasirin Rasha

Wannan mataki da aka daɗe ana sa rai tun bayan da gwamnatin mulkin sojin Nijar ta bukaci a yi hakan, na zama wani gagarumin ci gaba ga Rasha wadda ke kara mayar da hankali kan nahiyar Afirka da kuma goyon bayan gwamnatocin sojoji da suka yi juyin mulki a Nijar da makwabtanta Mali da kuma Burkina Faso.

Jami’an sun amince cewa tawagar Amurka za ta nufi Yamai babban birnin kasar nan da kwanaki kadan domin shirya janyewar cikin tsari. Tun da farko gidan talabijin na Jamhuriyar Nijar ya sanar da cewa jami'an Amurka za su kai ziyara mako mai zuwa.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ba ta sanar da matakin kai tsaye ba, kuma jami'ai sun ce har yanzu ba a kayyade lokacin janye sojojin ba.

Ƙwancen ƙetare da Nijar

Nijar ta dade tana kan gaba a bakoncin dabarun Amurka da Faransa na yakar masu ikirarin jihadi a yammacin Afirka, inda Amurka ta gina wani sansani a garin Agadez da ke cikin hamada kan kudi dalar Amurka miliyan 100 don sarrafa kuraman jiragen saman yaki da leken asiri.

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken a watan Maris din shekarar 2023 ya zama Ba’amurke mafi girma da ya taba ziyartar Nijar, inda ya sha alwashin tallafawa tattalin arzikin daya daga cikin kasashe mafi talauci a duniya da kuma neman goyon bayan zababben shugaban kasar Mohamed Bazoum, wanda ke zama babban aminin kasashen Yamma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.