Isa ga babban shafi

Kungiyar tsaffin 'yan tawayen Nijar sun ba da goyon bayansu akan korar sojin Amurka daga kasarsu

Kungiya Tsaffin 'yan tawayen arewacin Jamhuriya Nijar Sun goyi bayan matakin Majalisa sojin Nijar ta CNSP na kawo karshen yarjejeniya Soji tsakanin Kasar da Amruka.

Wasu sojoji a sanssanin dakarun Amurka da ke Jamhuriyar Nijar kenan.
Wasu sojoji a sanssanin dakarun Amurka da ke Jamhuriyar Nijar kenan. © AFP
Talla

 

Tsaffin 'yan tawayen wadanda suka hade a cikin wani kwamitin 'yan Sakai don kishin kasa

 UNVP, Sun fitar da Sanarwa ne yau Asabar 30 Maris a garin Agadas.

Da farko, kwamitin ya jinjinawa Shugaban Sojojin Janar Abdourahmane Tiani kan wannan matakin na yanke yarjejeniya Sojin da Amruka wadda suka ce Bata mutunta dokokin Kasar Jamhuriya Nijar ba.

Kwamitin na UNVP ya bayyana takaicin sa kan yadda sansanin Sojin Amruka dake mazaunin sa a Agadas bai taimaka da komai wajan rage hare-haren ta'adanci da aika-aika 'yan bindiga.

Kungiya Tsaffin 'yan tawayen ta kuma soki yadda Aka tilastawa 'yan kasar Kasar biyan kudaden shawagi da Jiragen sama Amuruka keyi na tabbata da tsaro Sabanin yadda yake wakana tsakanin Amruka da Djibouti.

Sanan Sun bukaci Gwamnati Sojin da ta gaggauta Bada Umurnin ga sojojin na su tattara nasu Yana su su fice daga Kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.