Isa ga babban shafi

Chadi ta umurci Amurka ta dakatar da aiki a wani sansanin soji a ƙasar

Babban hafsan sojin saman Chadi ya umarci Amurka da ta dakatar da ayyukan da ake yi a wani sansanin sojin sama dake kusa da N'Djamena babban birnin kasar, kamar yadda wata wasika da aka aike wa gwamnatin rikon kwarya da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya gani.

Babban hafsan sojin saman Chadi ya umarci Amurka da ta dakatar da ayyukan da ake yi a wani sansanin sojin sama dake kusa da N'Djamena babban birnin kasar, kamar yadda wata wasika da aka aike wa gwamnatin rikon kwarya da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya gani.
Babban hafsan sojin saman Chadi ya umarci Amurka da ta dakatar da ayyukan da ake yi a wani sansanin sojin sama dake kusa da N'Djamena babban birnin kasar, kamar yadda wata wasika da aka aike wa gwamnatin rikon kwarya da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya gani. © NEXTA
Talla

 

A cikin wasikar mai dauke da kwanan wata 4 ga watan Afrilu ministan tsaron kasar Chadi, babban hafsan sojin sama Idriss Amine Ahmed ya ce ya shaidawa jami'an tsaron Amurka da su dakatar da ayyukan da su ke yi a sansanin jiragen sama na Adji Kossei bayan da suka kasa gabatar da shaidar da ke basu izinin kasancewarsu a can.

Babban jami’in ya ce Yarjejeniyar tallafawa da kayan aiki da ma'aikata ba su wadatar ba.

Ya zuwa yanzu dai kasar Chadi ba ta sanar da bin sahun  Burkina Faso da Mali da kuma Nijar ba wajen kawo karshen hadin gwiwar soji da Faransa da sauran kawayenta na yammacin Turai, yayin da suke karfafa alaka da Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.