Isa ga babban shafi

Alkaluman mutanen da ambaliya ta kashe a Kenya ya karu zuwa 188

Ma’aikatar harkokin cikin gida a Kenya ta sanar da karuwar alkaluman mutanen da ambaliyar ruwa ta kashe a kasar zuwa mutum 188 dai dai lokacin da kasar ke ci gaba da fama da zubar kakkarfan ruwan sama ba kakkautawa.

Ambaliyar ruwan na ci gaba da tsananta a sassan kenya.
Ambaliyar ruwan na ci gaba da tsananta a sassan kenya. AP - Patrick Ngugi
Talla

Sassa da dama na kasar ta gabashin Afrika ne yanzu haka ke fama da zubar kakkarfan ruwan sama baya ga ambaliyar ruwa da kuma zaftarewar kasa, wanda ya lalata tituna da kadoji da kuma tarin abubuwan more rayuwa.

Sanarwar da ma’aikatar harkokin cikin gida ta kasar ta fitar a Alhamis dinnan ta ce mutane 188 ne suka mutu sakamakon ibtila’n ambaliyar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa mutane 125 ne suka jikkata yayinda wasu 90 suka bace a bangare wasu dubu 165 suka rasa muhallansu.

A wani ibtila’I na daban gomman mutanen kauyukan da ke gab da yankin Mai Mahiu na lardin Rift Valley ne suka rasa rayukansu bayan ballewar wata madatsar ruwa a tazarar kilomita 60 daga arewacin birnin Nairobi fadar gwamnatin kasar.

Ma’aikatar cikin gidan ta Kenya ta ce an yi nasarar gano gawarwakin mutane 52 yayinda har yanzu ake neman wasu 51 bayan ballewar madatsar ruwan.

Ko a jiya Laraba, ‘yan yawon bude ido fiye da 100 ne suka makare vayan ballewar kogin sakamakon tumbatsarsa a gandun dabbobin Maasai mara na kasar bayan kakkarfan ruwan saman.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, masu aikin ceto sun yi nasarar kwashe mutane 90 daga Masai Mara ta hanyar amfani da jirage da kuma motoci yayinda wasu 19 aka basu matsuguni bayan tumbatsar ruwan Talek.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.