Isa ga babban shafi
Amurka-Chadi

Amurka ta bai wa Chadi motoci da kwale-kwale don yakar ta'addanci

Kasar Amurka ta bai wa Chadi motocin soji da kwale kwale da kudin su ya kai kusan Dala miliyan guda da rabi domin yaki da Yan ta’adda.

Tallafin dai na da nufin agazawa kasar ta Chadi yakar ayyukan ta'addanci a yankin da ke fuskantar barazana daga Boko Haram da kuma kungiyar IS.
Tallafin dai na da nufin agazawa kasar ta Chadi yakar ayyukan ta'addanci a yankin da ke fuskantar barazana daga Boko Haram da kuma kungiyar IS. REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

Samantah Hero, mai Magana da yawun rundunar sojin Amurka da ke aiki a Afirka, ta ce barazanar kungiyar boko haram da IS na zuwa ne ta ruwa da kuma kasa daga tafkin Chadi da Arewa maso Gabashin Najeriya.

Jakadan Amurka a Chadi, Richard K. Bell ya ce taimakon ya hada da motoci 6 da kwale kwale 6, yayin da sojojin Chadi 13 yanzu haka su ke samun horo a Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.