Isa ga babban shafi
Tafkin Chadi

Kungiyoyin agaji 6 sun janye daga yankin Tafkin Chadi

Majalisar Dinkin Duniya ta ce hare-haren mayakan Boko Haram, sun tilastawa kungiyoyin bada agaji da dama dakatar da ayyukansu a yammacin yankin Tafkin Chadi, lamarin da ya jefa dubban mutane cikin halin kunci na rashin abinci da kuma samun kulawar lafiya tsawon makwanni.

Wani sashi na yankin Tafkin Chadi.
Wani sashi na yankin Tafkin Chadi. REUTERS/Emmanuel Braun
Talla

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya ta ce sama da ‘yan gudun hijirar dubu 150,000 ne suka dogara akan taimakon kayan abinci da magunguna da kungiyoyin agaji ke samar musu domin rayuwa a sansanoninsu dake yankin tafkin na Chadi.

Ofishin bada gajin jin kai na Majalisar dinkin duniya OCHA, ya ce zuwa yanzu akalla manyan kungiyoyin agaji shidda ne suka dakatar da ayyukansu, biyo bayan hare-haren kungiyar Boko Haram a yankunan da suke aiki a watan Satumban da ya gabata da kuma farkon Oktoban da muke ciki.

Koda yake ofishin bada agajin jin kan na OCHA, ya kaucewa bayyana sunayen kungiyoyin agajin, hukumar samar da abinci ta majalisar dinkin duniya WFP, ta ce tana daga cikin wadanda suka janye ayyukan nasu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.