Isa ga babban shafi

Ƙasashen yamma na taka-tsantsan yayin da ake shirin zaɓe a Chadi ranar Litinin

A ranar Litinin mai zuwa ne za a gudanar da zaben shugaban ƙasa a Chadi, lamarin da ya sa ta kasance ta farko a ciki jerin ƙasashen da sojoji ke mulki a tsakiya da yammacin Afrika da za a yi zabe bayan shafe shekaru a ƙarkashin mulkin soji.

Shugaban Chadi,, Mahamat Idriss Deby Itno.
Shugaban Chadi,, Mahamat Idriss Deby Itno. © Denis Sassou Gueipeur / AFP
Talla

A yayin da tuni ƴan adawa ke zargin shirin tafka magudi, ɗan takarar da ake hasashen zai lashe wannan zaɓe shi ne shugaban ƙasar mai ci, Janar Mahamat Idriss Deby Itno, wanda  ya karɓe mulki jim kaɗan bayan da ƴan tawaye suka bindige mahaifinsa har lahira a filin daga a cikin watan Afrilun shekarar 2021.

Masu sharhi dai sun ce ƙawayen Chadi na yammaci Turai sun yi shuru sun zuba ido tare da fatan aƙalla zaben zai samar da gwamnatin dimokaradiyya.

Chadi ce ƙasa ta ƙarshe a yankin Sahel da ke da alaƙa da dakarun Faransa a halin da ake ciki, bayan da makwaftanta, Mali, Nijar da Burkina Faso, waɗanda ke ƙarkashin mulkin soji suka sallami Faransa da sauran manyan ƙasashen yamma daga ƙasashensu.

Yanzu masu sharhi sun yi itifakin cewa, abin da ke gaban ƙasashen yama a game da Chadi yanzu shine tabbatar da kwanciyar hankali a ƙasar, tare da jaddada matsayinsu a cikin ta, a daidai lokacin da Rasha ke neman gindin zama a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.