Isa ga babban shafi

Yan adawa a Chadi na zargin tsagin gwamnati da fara yakin neman zabe kafin lokaci

Yan adawa a Chadi na ci gaba da nunawa gwamnati ‘yatsa kan zarginta da take musu hakkokin tsayawa takara da kuma walwalawa a fagen na siyasa dai-dai lokacin da aka fara nuna alamun fara gangamin yakin neman zabe.

Shugaban gwamnatin sojin Chadi Mahamat Idris Deby
Shugaban gwamnatin sojin Chadi Mahamat Idris Deby © AFP
Talla

Bayanai sun ce tuni manyan biranen kasar suka cika da hotunan ‘yan takara cikin kuwa har da jagoran gwamnatin sojin kasar na yanzu Mahamat Idris Deby Itno.

Bisa ka’ida dai ranar 14 ga watan Afrilun da muke ciki ne ya kamata a fara yakin neman zaben a hukumance, sai dai kuma dukannin alamun sun nuna cewa magoya bayan shugaban sun yi gajen hakuri.

A zantawar sa da manema labarai, guda daga cikin ‘yan takarar da aka haramtawa tsayawa neman zaben Nasra Djimasgar ya ce manyan hotunan da ‘yan siyasar suka fara kafewa a kan manyan titunan kasar da kuma yadda hotunansu ke yawo cikin unguwanni ya nuna yadda suka fara gangamin yakin neman zaben a fakaice.

Tuni dai jama’ar kasar suka fara nuna sha’awar su ga ‘yan takara da kuma fadin albarakacin baki, al’amarin da bashi da maraba  da yakin neman zabe

Nasra ya kuma ce wannan na nufin shugaba Mahamat na amfani da karfin Iko wajen yunkurin kwashe kwanaki 35 yana yakin neman zabe a maimakon kwanaki 21 da doka ta kayyade.

Jama’ar Chadi zasu fara kada kuri’ar zaben shugaban kasa ne a ranar 6 ga watan Mayun da muke ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.