Isa ga babban shafi

Gwamnatin sojin Chadi ta tabbatar da tsare wani hamshakin attajirin kasar

Hukumomi a kasar Chadi sun tabbatar da tsare wani hamshakin attajirin kasar Ibrahim Hissein Bourma, kwanaki uku bayan bacewarsa da ya haifar da ce-ce-ku-ce a kasar. A ranar Asabar din nan gwamnati ta tabbatar da cewa an kama shi bisa umarnin kotu.

'Yan sandan Chadi na sintiri a Ndjamena
'Yan sandan Chadi na sintiri a Ndjamena BRAHIM ADJI / AFP
Talla

Tun kafin sanarwar gwamnati, wani kwamitin goyon baya da bin diddigin bacewarsa da aka kafa cikin gaggawa, ya tabbatar da cewa wasu mutane sanye da kakin sojoji a cikin motoci dauke da muggan makamai ne suka yi garkuwa da shi daga gidansa da misalin karfe 2:30 na daren Laraba wayewar Alhamis.

Za'a iya kashe shi

Iyalansa da makusanta sun shiga fargaba, saboda matakin kama shi na zuwa ne kwanaki kadan bayan sanarwar da dan uwansa Ousmane Hissein Bourma, wanda ya ce ya kafa sabuwar kungiyar tawaye da nufin yakar gwamnatin rikon kwaryar soji ta Mohammed Deby.

Tun bayan ɓatarsa hukumomi sun yi shiru har zuwa daren Asabar, inda a karshe suka amince da kama shi.

Kakakin gwamnan sojin kasar Abdrame Koulamallah da ya tabbatar da kama attajirin, ya ce ana bincikensa kan wasu makamai da aka ɓoye a gidansa.

"Ba a yi garkuwa da wannan mutumin ba, an kama shi ne karkashin kulawar mai gabatar da kara, wanda ya kaddamar da bincike kan bayanan sirri daga jami'an leken asirin kan wasu makaman da aka boye a gidansa”

Jami’in ya ce an gano bindigogin yaki guda ashirin da biyar, da makamin roka, da motar sulke, da mota dauke da manyan makami da ma makudan kudaden na dala a gidansa.

Ina ake tsare da shi? Me yasa aka kama shi cikin dare? Tambayoyi kenan da Abdremane Koulamallah ya ce kutu ce kadai za ta yi bayani.

Kusanci da Deby

A shekaru 35, Ibrahim Hissein Bourma shi ne tsohon darektan tallace-tallace na Société des hydrocarbures du Tchad, wata kamfanin man fetir na kasar.

Ya fito daga ɗaya daga cikin iyalai mafi arziki a Ndjamena, kuma ya tara dukiya ta kamfanoninsa na gine-gine da na motoci da kuma tufafi, wanda  masu lura da al’amura a Chadi suka ce kasuwancinsa ya bunƙasa ne sanadiyar kusancisa da tsohon shugaban kasar marigayi Idriss Deby Itno, saboda matansu ‘yan uwan juna ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.