Isa ga babban shafi
SAKAMAKON ZABE

Jam'iyya mai mulkin Togo ta samu rinjaye a majalisun dokokin kasar

Hukumar zabe ta kasar Togo ta tabbatar da Jam’iyya mai Mulki a matsayin wacce ta lashe kaso mai tsoka na kujerun ‘yan Majalisu a zaben da aka gudanar a watan Afrilun da ta gabata.

Yadda ma'aikatan zabe ke shirin kirga kuri'un da aka kada a birnin Lome ranar 29 ga Afrilu, yayin zaben 'yan majalisar dokokin kasar Togo.
Yadda ma'aikatan zabe ke shirin kirga kuri'un da aka kada a birnin Lome ranar 29 ga Afrilu, yayin zaben 'yan majalisar dokokin kasar Togo. © Émile Kouton / AFP
Talla

Wannan dai na zuwa ne bayan majalisar ta sha caccaka daga ‘yan kasar kan sauya fasalin kundin tsarin mulkin Togon da zai ba wa Shugaba Faure Gnassingbe damar tsawaita wa’adin mulkinsa.

Kamar yadda hukumar ta fitar da sakamakon zaben, ya nuna cewa Jam’iyyar Gnassingbe mai suna Union for the Republic party ta na da kujeru guda 108 cikin 113 a cikin zauren Majalisar.

Kamar yadda aka tabbatar a cikin sabuwar dokar a watan Afrilun wannan shekarar, Gnassingbe shi ne zai zama shugaban gwamnatin Togo, mukamin dake daidai da Firaminsta.

Faure Gnassingbe da ya kusan shafe shekaru 20 yana kan karagar Mulki dai ya gaje shi daga wurin mahaifinsa Gnassingbe Eyadema da ya shafe shekaru 40 yana Mulki a kasar dake a Yammacin Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.