Isa ga babban shafi

Tallafin kasa da kasa ya fara isa Libya bayan salwantar dubban rayuka

Kasashe da dama ne suka amsa kiran da Libya ta yi musu na bukatar agajin gaggawa, domin taimaka wa dubban al’ummar kasar da ambaliyar ruwa ta shafa, wadda ya zuwa yanzu aka tabbatar da ta kashe sama da mutane dubu 5, yayin da wasu dubbai suka bace.

Wani sashin birnin Derna da ambaliyar ruwa ta afka wa a kasar Libya.11 Satumba, 2023.
Wani sashin birnin Derna da ambaliyar ruwa ta afka wa a kasar Libya.11 Satumba, 2023. © Press Office of Libyan Prime Minister / AFP
Talla

Akalla kasashe 13 ne suka aike da tawagar masu kai agajin gaggawa ga Libya ko kuma suke kan shirin aikewa da tallafin, don ceto dubun dubatar mutanen da iftila’in ambaliyar ruwan ya tagayyara.

Tuni dai jiragen saman Qatar biyu makare da kayayyakin agaji suka sauka a birnin Bengazi tun da safiyar ranar Laraba, yayin da Turkiya ke shirin aikewa da jiragen sama uku tare da tawagar jami’na agaji 168 da kuma kananan jiragen ruwa 2.

Italiya kuwa jami’na kwana-kwana take shirin aika wa zuwa kasar ta Libya, yayin da tuni na Spain suka bazama zuwa sassan kasar.

Haddadiyar Daular Larabawa ta aike da jiragen sama biyu dauke ton 150 na kayayyakin abinci, da magunguna, irin matakin da Algeria, da Kuwait, da kuma Jordan suka dauka, yayin da Masar ke shirin bin sawu.

Majalisar dinkin duniya kuwa, shirin samar da tallafin abinci take ga akalla iyallai dubu 5 da suka rasa matsugunansu a Libyan, yayin da kungiyar EU ta sanar da  ware euro dubu 500, a matsayin tallafi ga al’ummar kasar, sai kuma Faransa da ta aike da jami’an lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.