Guguwar Belal ta haddasa ambaliyar ruwa a sassan Maurituis
Ambaliyar ruwa ta afka wa wasu sassan Mauritius sakamakon kakkarfar guguwar da ta isa kasar da ta kasance tsibiri a wani bangaren tekun India.
Wallafawa ranar:
Hotunan da aka yada ta kafafen sada zumunta sun nuna yadda motoci masu yawan da ke kan manyan hanyoyin Port Louis babban birnin kasar ta Maurituis suka nutse a ambaliyar ruwan, yayin da kuma ruwan laka hade tarin shara ya mamaye unguwannin birnin a daidai lokacin da ruwan sama kamar da bakin kwarya ke ci gaba da shatata.
Mahukuntan Maurituis din sun ce ya zuwa lokacin wannan wallafa mutum guda ne ya rasa ransa, tare da gargadin cewa adadin ka iya karuwa sakamakon guguwar Belal da ta akfa musu cikin tsala karfin gudun da ya kai na kilomita 130 a sa’a guda.
Kididdiga ta nuna cewar sal goma zuwa sha biyu kakkarfar guguwa ke afka wa sassan Mauritius a duk shekara a tsakanin Afrilun zuwa Nuwamba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu