Isa ga babban shafi

Adadin mutanen da suka mutu a ambaliyar Somalia ya kusan 100

Adadin mutanen da suka mutu sakamakon ambaliyar ruwan da ta auku bayan mamakon ruwan sama a Somalia ya kai 96, kamar yadda  kamfanin dillancin labaran kasar ya ruwaito  a Asabar dinnan

Wasu sassan birnin Mogadishu da ambaliya ta mamaye.
Wasu sassan birnin Mogadishu da ambaliya ta mamaye. REUTERS - FEISAL OMAR
Talla

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta kasar, Mahamuud Moallim ya tabbatar da adadin ta wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X.

Kamar sauran kasashen da ke yankin kuryar gabashin Afrika, Somalia ta fuskanci ruwan sama kamar da bakin kwarya a watan Oktoba, sakamakon matsalar sauyin yanayi.

Ambaliyar, wadda aka bayyana a matsayin mafi muni a cikin gwamman shekaru, ya daidaita kimanin mutane dubu dari 7 a cewar  Majalisar Dinkin Duniya.

Mamakon ruwan sama da aka yi a fadin kasar ya haddasa ambaliyar da ta daidaita, tare da tagayyara dimbim mutane, abin da ya tsananta matsalar jinkan da kasar ke fama da ita  sakamakon shekaru da ta  kwashe tana yaki da  ‘yan ta’adda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.